An Shiga Tashin Hankali a Jihar Filato, Wani Soja Ya Kashe Direban Adaidaita Sahu

An Shiga Tashin Hankali a Jihar Filato, Wani Soja Ya Kashe Direban Adaidaita Sahu

  • Wani soja ya kashe direban adaidaita sahu a bakin kofar barikin sojoji na Rukuba Jos, jihar Filato bayan wata 'yar hatsaniya
  • Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce direban adaidaitan ya taka kafar sojan bisa kuskure amma soja ya daba masa wuka
  • Rundunar sojin Najeriya ta kama sojan da ya aikata laifin, kuma ta ce za ta tabbatar da an yi adalci a yayin da ta soma bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Wani soja da ke a barikin sojoji na Rukuba, Jos, ya dabawa direban adaidaita sahu wuka har lahira a bakin kofar barikin.

Lamarin ya faru a Gebu-Bassa da misalin karfe 7:00 na yamma, yayin da mamacin mai suna Abdullahi Muhammad ya tsaya siyan kaya a kusa da kofar barikin.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda ya samawa 'yan jiharsa ayyukan tarayya masu yawa

Sojoji sun magantu yayin da wani soja ya kasshe direban adaidaita sahu a Jos
Sojan Najeriya ya kashe direban adaidaita sahu a Jos, jihar Filato. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Soja ya kashe direban adadaita a Jos

Shugaban GAFDAN, Garba Abdullahi, ya ce rikici ya fara ne bayan Abdullahi ya taka kafar sojan yayin da yake ja da baya da adaidaitarsa inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Marigayin ya ba da hakuri bayan lamarin. Amma sojan, wanda ke sanye da kayan gida, ya mare shi, abin da ya haifar da musayar yawu."

- A cewar Garba Abdullahi.

Daga nan sai sojan ya dauko wuka ya soka wa Abdullahi a kirjinsa. An garzaya da shi asibitin barikin, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

Mahaifin direban adadaita ya koka

Garba Abdullahi ya yi Allah-wadai da kisan, yana kira ga sojojin Najeriya da su tabbatar da adalci ga marigayin.

Alhaji Muhammad, mahaifin mamacin, ya nemi a dauki matakin da ya dace, yana kira ga shugabannin soja su hukunta wanda ya aikata laifin.

Kakakin rundunar soji ta uku, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai mika ta'aziyyarsa ga iyalin mamacin.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da jirgin kasa ya murkushe wata mota a Legas, mutane sun magantu

Rundunar soji ta magantu kan lamarin

Laftanar Kanar Aliyu ya ce:

“Rahotanni na farko sun nuna cewa musayar yawu tsakanin sojan da Abdullahi ta rikide ta zama fadan da ya kai ga wannan abin takaici."

Danja ya ce tuni aka kama sojan da ya aikata laifin, kuma ana gudanar da bincike don gano musabbabin lamarin.

“Rundunar sojojin Najeriya za ta tabbatar da gaskiya da adalci. Idan aka same shi da laifi, za a dauki matakin ladabtarwa bisa ka'ida."

- A cewar Laftanar Kanar Danja.

Matasa sun yi wa soja jina jina

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu fusatattun matasa da ke sana'ar acaba sun yi wa wani soja jina jina yayin da suka kashe wani mutum a Ogun.

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin, inda aka gano cewa matasan sun kona mutumin har lahira saboda zargin satar babur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.