Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Shugaban Ƴan Bindiga da Yaransa a Katsina
- Sojojin Najeriya sun kashe Alhaji Ma’oli, wani hatsabibin shugaban 'yan ta’adda da ya addabi garuruwan Katsina da kewaye
- Mazauna yankin sun godewa dakarun sojin saboda kokarin da suke yi wajen kawo zaman lafiya da tabbatar da tsaro a yankinsu
- A Zamfara kuwa, dakarun sojin sun kashe Kachalla Muchelli, shugaban sansanin 'yan bindiga na Kuchi Kalgo a wani farmaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Sojojin Operation Fansan Yamma sun ci gaba da kai farmaki kan 'yan ta’adda a Arewa maso Yamma, suka kashe da dama a Katsina da Zamfara.
A jihar Katsina, dakarun sun kai farmaki a kauyen Mai Sheka, garin Kunchin Kalgo, inda suka kashe wasu 'yan ta’adda ciki har da Alhaji Ma’oli.
Zagola Makama, wani babban mai sharhi kan harkokin tsaron Najeriya ne ya fitar da wannan rahoton a shafinsa na X a ranar 26 ga Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe shugaban 'yan bindiga a Katsina
Rahoton ya nuna cewa Alhaji Ma’oli yana da hannu wajen karbar haraji da aikata laifuffuka a Unguwan Rogo, Mai Sheka, Magazawa da sauran wurare.
Wannan farmakin ya tarwatsa kungiyar 'yan ta’addan Alhaji Ma'oli, inda ya kawo sauki ga mazauna yankin da suka dade suna shan azaba a hannunsa.
Mazauna yankin Bilbis sun nuna godiya ga jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi wajen maido da zaman lafiya a yankunansu.
Zamfara: Sojoji sun kashe Kachalla Muchelli
A Zamfara kuwa, dakarun Counter Terrorism Team 7 (CT 7) sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a kan hanyar Bilbis-Danjigba ranar 25 ga Disamba.
A wannan gumurzu, Kachalla Muchelli, shugaban sansanin 'yan ta’adda na Kuchi Kalgo, ya gamu da ajalinsa.
Majiyoyin soji sun tabbatar da cewa waɗannan hare-haren suna cikin kokarin kawar da 'yan ta’adda da 'yan bindiga a yankin.
Sojoji sun kashe shugaban 'yan bindiga "Al'jan"
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga, 'Al'jan' da ya addabi garuruwan jihar Zamfara da kewaye.
"Al'jan" wanda ba a san ainahin sunansa ba, an ce ya gamu da ajalinsa a wani harin kwanton bauna da sojoji suka kai masa da yaransa a tsakanin Mada da Yandoton Daji da ke Tsafe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng