Muhimman Dalilai 4 da Suka Sa Ɗangote da NNPCL Suka Rage Farashin Fetur a Najeriya

Muhimman Dalilai 4 da Suka Sa Ɗangote da NNPCL Suka Rage Farashin Fetur a Najeriya

  • Matatar Ɗangote da kamfanin mai na kasa watau NNPCL sun rage farashin litar fetur daga sama da N1,000 zuwa N899 a makon da ya shige
  • Wannan mataki dai ya jawo saukar farashin fetur zuwa ƙasa da N1,000 a gidajen man ƴan kasuwa a faɗin ƙasar nan
  • Legit Hausa ta tattaro maku muhimman dailin da suka sa aka fara samun sauƙin tsadar fetur wanda ke shafar farashin kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A makon jiya ne matatar hamshaƙin attajirin nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta sanar da rage farashin litar man fetur ga ƴan kasuwa domin saukakawa ƴan Najeriya.

Wannan mataki dai ya yi wa ƴan Najeriya daɗi musamman saboda halin tsadar rayuwa da ake fama da ita, wanda tsadar fetur na ɗaya daga cikin abubuwan da suka haifar da hakan.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi lakanin dake ruguzo da farashin man fetur a Najeriya, ya jero dalilai

NNPCL.
Abubuwan da suka jawo saukar farashin man fetur a Najeriya Hoto: NNPCLimited
Asali: Getty Images

Masana sun bayyana cewa matakin da matatar Ɗangote ta ɗauka zai kara haifar da gasa a kasuwancin mai, wanda ka iya zama sanadin ƙara rage farashin lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur

A wata sanarwa da rukunin kamfanonin Ɗangote watau Ɗangote Group ya wallafa a shafin X ranar Alhamis, 19 ga Disamba, ya ce an rage farashin litar fetur zuwa N899.

Sanarwar ta ce an rage farashin man ne domin sauƙaƙawa ƴan Najeriya a lokacin da suke tunkarar bukukuwan kirismeti da sabuwar shekara.

"Domin rage tsadar sufuri, Dangote ya sauke farashin lita, Daga yau, man feturinmu zai kasance a farashin N899.50 kowace lita a tashar lodin motoci," in ji sanarwar.

Kamfanin NNPCL ya bi sahun matatar Ɗangote

Kwanaki biyu bayan haka, kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya rage farashin litar mansa daga N1,020 zuwa N899 kamar dai yadda matatar Ɗangote ta yi.

Ƙungiyar masu kasuwancin man fetur (PETROAN) ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, 21 ga watan Disamba, 2024, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a fitacciyar kasuwa, ta lakume shaguna masu yawa

Mai magana da yawun PETROAN, Dr Joseph Obele, ya nuna cewa farashin ka iya ƙara raguwa kafin ƙarshen watan Janairu 2025, duba da faɗuwar farashin ɗanyen mai da farfaɗowar Naira.

Dalilin rage farashin man fetur a Najeriya

Faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, farfaɗowar Naira a kasuwar canji na daga cikin abubuwan da suka taka rawa aka samu sauƙin tsadar mai.

Legit Hausa ta tattaro maku dukkan dalilin da suka jawo samun rangwamen fetur a Najeriya, ga su kamar haka:

1. Yanayin kasuwa

Idan ba ku manta ba, gwamnatin tarayya ta tsame hannunta a harkokin ƙayyade farashin man fetur bayan cire tallafi, ta saki lamarin sai yadda kasuwa ta kaya.

A wata hira da Arise tv, shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce yanayin kasuwa ne ya sa mai ya fara sauka.

Ɗangote ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen kare muradan matatar da ya gina wanda ya zuba ma jari mai nauyi tare da tabbatar da komai ya tafi yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Matatar Ɗangote za ta fara sayar da fetur ga yan Najeriya, ta faɗi sabon farashin lita

"Bari na faɗi haka kawai, an samu wannan ragi ne saboda yanayin da kasuwa ta tsara," in ji shi.

2. Faɗuwar ɗanyen mai a duniya

Faɗuwar darajar ɗanyen man fetur a kasuwar a duniya a ƴan makonnin nan zuwa $70 kan kowace ganga na cikin dalilan da ake ganin sun kawo sauki a farashin fetur.

Reauters ta wallafa rahoton cewa duk da farashin gangar mai ya motsa ranar Juma'a, da yiwuwar ya ƙara ƙasa a 2025 saboda rikicin Rasha da Ukraine da na Syria.

3. Darajar Naira a kasuwar canji

Abu na uku da ake ganin ya taka muhimmiyar rawa shi ne farfaɗowar da Naira ke yi kan Dalar Amurka a kasuwar hada-hadar kuɗi.

A ƴan makonnin da suka shiga sai da Naira ta rage akalla N200, koowace Dalar Amurka ta dawo kimanin N1,500 a kasuwar bayan fage.

Kafin samun wannan ci gaban, Dalar Amurka ta kai kusan N1,800 a kasuwar ƴan canji amma lokaci guda ta sauka zuwa kimanin N1,500, rahoton Nairametrics.

Kara karanta wannan

Bayan umarnin Tinubu, jiragen ƙasa sun fara ɗaukar fasinjoji kyauta a Najeriya

4. Cinikin ɗanyen mai da Naira

Ana ganin fara hada-hadar ɗanyen mai a Naira tsakanin gwamnatin Najeriya da matatar Ɗangote ya taka muhimmiyar rawa wajen sauke farashin litar fetur.

Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yabi shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa tsarin cinikin ɗanyen mai a kudin Najeriya.

A wata sanarwa da Ɗangote Group ya wallafa a X, fitaccen ɗan kasuwar ya ce wannan tsari ya taka rawa wajen farfaɗo da tattalin arziki da rage farashin fetur.

Matatar Ɗangote ta matso kusa ga ƴan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Ɗangote ta ƙulla yarjejeniya da gidan man NRS domin fara sayar da fetur kai tsaye ga ƴan Najeriya.

A wata sanarwa da ta fitar, matatar ta ce tuni aka fara sayar da kowace litar mai kan N935 a gidajen man MRS a Legas kuma nan ba da jimawa ba kaya za su isa sassan ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262