Kwankwaso Ya Tsokano APC, Ta Yi Masa Wankin Babban Bargo

Kwankwaso Ya Tsokano APC, Ta Yi Masa Wankin Babban Bargo

  • Jam'iyyar APC ba ta ji daɗin kalaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ba na rage mata tasiri a jihar Kano a zaɓen 2027
  • Shugaban APC na jihar Kano, ya caccaki Kwankwaso inda ya bayyana kalaman na sa a matsayin abin dariya
  • Abdullahi Abbas ya buƙaci madugun na Kwankwasiyya da ya farka daga mafarkin da yake domin har yanzu APC ce zaɓin jama'a a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi martani mai zafi ga madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

APC ta yi watsi da iƙirarin da tsohon gwamnan na jihar Kano, ya yi na cewa zai rage yawan ƙuri’unta a jihar a zaɓen 2027.

APC ta caccaki Kwankwaso
APC ta yi wa Kwankwaso martani Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na Kano, Abdullahi Abbas ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

2027: Kwankwaso ya kada hantar Ganduje, ya fadi shirinsa kan APC a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani APC ta yi wa Kwankwaso?

Ya bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin abin dariya, inda ya yi kira gare shi da ya mayar da hankali wajen ganin ya zama cikakken mamba a jam'iyyar NNPP, wacce aka ce an kore shi daga cikinta.

Abdullahi Abbas ya bayyana Kwankwaso a matsayin “ɗan gudun hijirar siyasa,” inda ya zarge shi da zama ƙarfen ƙafa ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, a ƙoƙarin da ya ke na ci gaba da taka rawa a siyasar Najeriya.

"Muna kira ga Kwankwaso da ya daina mafarki ya fuskanci gaskiya. Ƙwarin gwiwar da ya nuna na rage ƙuri’un APC a jihar Kano ba komai ba ne illa tunani irin nasa. Har yanzu jam’iyyarmu ita ce zaɓin jama'a."
"Magoya bayan mu a APC ba su da wani dalilin da zai sa su damu da Kwankwaso, wanda aka kore shi daga jam’iyyar NNPP, saboda rashin sanin ya kamata da son kai. Yanzu ya ba shi ga tsutsu ba shi ga tarko a fagen siyasa."

Kara karanta wannan

PDP ta ƙara rasa babban Jigo, dan Majalisa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

"Kwankwaso ya bar APC ne saboda ya kasa aminta da manufofinmu na ci gaba. Girman kansa ya ya tilasta masa barin PDP. Yanzu ma jam’iyyar NNPP ta yi watsi da shi, ya zama baya da gida a siyasa."

- Abdullahi Abbas

Kwankwaso ya faɗi mai jawo matsala a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon kwamishina a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana mai haddasa rigima a jihar.

Alhaji Musa lliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ne ke haddasa rigima a Kano ba Abdullahi Umar Ganduje ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng