Gwamna Ya Sha da Kyar a Hannun 'Yan Fashi? 'Yan Sanda Sun Yi Bayani

Gwamna Ya Sha da Kyar a Hannun 'Yan Fashi? 'Yan Sanda Sun Yi Bayani

  • Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta fito ta yi martani kan harin da ake cewa ƴan fashi da makami sun kai wa tawagar Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana rahotannin da aka yaɗa a kan harin a matsayin ƙarya tsagwaronta
  • Moris Dankwambo ya buƙaci masu amfani da shafukan sada zumunta da su riƙa tantance labaransu kafin su gayawa duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta yi martani kan batun cewa ƴan fashi da makami sun farmaki tawagar Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.

Rundunar ƴan sandan ta yi watsi da iƙirarin cewa ƴa fashi da makami, sun kai wa ayarin motocin gwamna Ahmadu Fintiri hari a jihar Taraba.

'Yan sanda sun musanta kai hari kan gwamnan Adamawa
'Yan sanda sun musanta harin 'yan fashi kan gwamnan Adamawa Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Moris Danwambo, ya ƙaryata rahotannin kai harin a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

"Ba 'yan bindiga ba ne": Shugaban hukuma ya fadi abin da ya fi hallaka 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ƴan sanda suka ce kan farmakar Gwamna Fintiri?

Moris Dankwambo ya bayyana rahotannin da aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta game da harin da aka kai kan ayarin gwamnan, a matsayin ƙarya tsagwaronta.

Kwamishinan ƴan sandan ya ce gaskiyar lamarin ita ce, a ranar 19 ga watan Disamba, motar jami’an tsaro da ke cikin ayarin motocin gwamnan, yayin da suke dawowa daga jihar Taraba, sun ci karo da wani shingen da ƴan fashi suka kafa.

Ya bayyana cewa a bisa tsarin kare manyan mutane, motar jami'an tsaron tana gaban ayarin motocin.

Ƴan sanda sun fatattaki ƴan fashi da makami

Ya ce jami'an tsaron suna isa inda lamarin ya faru, sun tarar cewa toshe hanyar ya tilastawa sauran matafiya dakatar da tafiya, tare da ajiye motoci a kan hanya.

Tawagar jami’an tsaro nan take suka mayar da martani inda suka fatattaki ƴan fashi da makamin, tare da tabbatar da ci gaba da zirga-zirgar duk masu ababen hawa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga, rayuka sun salwanta

Kwamishinan ƴan sandan ya yabawa jami’an tsaron kan ƙoƙarinsu, sannan ya yi kira ga masu amfani da shafukan sada zumunta da su riƙa tantance labarinsu kafin su bayyanawa jama'a.

Gwamna Fintiri ya ƙirƙiro masarautu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ƙara yawan masarautun da ake da su a jihar.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ƙirƙiro sababbin masauratu guda bakwai da sarakunansu domin inganta samar da zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng