Tinubu Ya Mika Sako ga Gwamnan Jigawa, Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Namadi
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika ta'aziyya ga gwamnatin jihar Jigawa bisa rasuwar mahaifiyar gwamna
- Hajiya Maryam Namadi ta koma ga Allah a ranar Laraba, inda aka yi jana'izarta ba tare da gwamna Umar Namadi ba
- Shugaba Tinubu ya shawarci iyalan Namadi da su dora a kan ayyukan alheri da ta rika yi a lokacin rayuwarta don tuna wa da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa - Shugaba Bola Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi.
Gwamnatin Jigawa ta sanar da rasuwar Hajiya Maryam a ranar Laraba, 25 ga Disamba, inda ta koma ga mahalicci a lokacin da gwamna Namadi ke wajen kasar.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa tuni aka yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci a tanada, an kuma binne ta a garinsu na Kafin Hausa a yammacin Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yi ta’aziyya ga Namadi
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi addu’ar samun rahama ga Hajiya Maryam Namadi, wacce ta koma ga mahaliccinta.
Ya mika sakon ta’aziyyar ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, inda ya yabawa kyawawan ayyukan ci gaba da ta yi a lokacin rayuwarta.
Tinubu ya zaburar da iyalan Namadi
Shugaban Najeriya ya nemi iyalan Hajiya Maryam Namadi da su ci gaba da ayyukan alherinta, don tabbatar da cewa sun bar kyakkyawan tarihi da za a tuna da ita.
A sakon ta’aziyyarsa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Gwamna Umar Namadi da sauran iyalan karin hakuri bisa babban rashi da aka yi masu, tare da tunawa da ita ta ayyukan alherinta.
Mahaifiyar gwamna Namadi ta rasu
A baya kun ji cewa gwamnatin Jigawa ta sanar da rasuwar mahaifiyar gwamna Umar Namadi, Hajiya Maryam Namadi, wacce ta kwanta dama a safiyar ranar Laraba.
Gwamna Umar Namadi ya bukaci addu'o'in jama'a domin nema wa mahaifiyarsa rahamar Allah SWT wacce ta rasu a jiya Laraba.
Asali: Legit.ng