Yadda Aminin Turji Ke Tsula Tsiyarsa, Wasu a Yankin Sokoto Sun Roki Gwamnati Alfarma
- Mazauna yankunan Idi da Ranbadawa a jihar Sokoto sun nemi gwamnati ta tsare su daga zaluncin Kallamu, wani aminin Bello Turji
- Kallamu ya mamaye yankin, yana mulkin kama-karya ba tare da tsoro ba, wanda ya jefa al’ummomin cikin firgici da rashin tsaro
- Mutanen gari na roƙon gwamnati ta gaggauta daukar matakin dawo da doka da oda don kare rayuka da dukiyoyinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Mazauna garuruwan Idi da Ranbadawa a yankin Gobir a jihar Sokoto sun roƙi hukumomi su tsoma baki don kubutar da su daga zalincin yan bindiga.
Mazauna garuruwan sun nuna damuwa kan halin da suke ciki kan zaluncin Kallamu, wani sanannen shugaban ‘yan fashi kuma aminin Bello Turji.
Yadda aminin Bello Turji ya addabi al'ummar Sokoto
Rahoton Zagazola Makama ya ce Kallamu ya zama kamar wani mai mulki a yankin, inda yake tafiyar da harkokinsa ba tare da tsoro ba, kuma ya mayar da hukumomin yankin ba komai ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mazauna yankin sun bayyana yadda Kallamu ke cin karensa babu babbaka tare da jagorantar ayyukan ta'addanci.
“Duk wanda ya gan shi yana yawo a Idi yana kama da wanda ya mallaki garin, ba wanda ya isa ya kalubalance shi."
- Cewar wani mazaunin yankin
Wasu majiyoyi sun nuna cewa Kallamu yana amfani da ikonsa wajen gudanar da aikace-aikacen laifuka a yankin.
An tabbatar da cewa ikonsa a yankin yana neman fin na gwamnati inda ya bar jama’a babu kariya ko damar neman adalci daga hukuma.
Ta'addanci: Mazauna Sokoto sun roki gwamnati alfarma
“Duk lokacin da ya zo gari, mutane ko dai su durƙusa masa saboda tsoro ko kuma su gudu don tsira da rayukansu, ya mamaye garinmu, kuma muna rayuwa a hannunsa."
- Cewar wata majiya
Al’ummomin Idi da Ranbadawa sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa don dawo da tsaro da kuma kare rayuka.
“Mun roƙi gwamnati ta ceto mu daga wannan masifa, babu inda muka samu mafaka, kuma rayuwarmu tana cikin hatsari kullum."
- Cewar wani dattijo a yankin
Yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto
Mun ba ku labarin cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin suna da alaƙa da Bello Turji sun yi garkuwa da matafiya a jihar Sokoto da ke yankin Arewa.
Ƴan bindigan waɗanda ke ta'addancinsu a gabashin Sabon Birni sun yi garkuwa da matafiyan a ranar Talata, 24 ga watan Disambar 2024.
Asali: Legit.ng