"Akwai Kullin Arziki a 2025," Ganduje Ya Nemi a Kara Yi wa Tinubu Uziri

"Akwai Kullin Arziki a 2025," Ganduje Ya Nemi a Kara Yi wa Tinubu Uziri

  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci 'yan Najeriya da su kara hakuri tare da yi wa gwamnati uziri
  • Ganduje ya bayyana haka ne ta cikin sakon taya Kiristocin Najeriya murnar bikin Kirisimeti, inda ya ce Tinubu ya damu da kasar nan
  • Tsohon gwamnan Kano ya bayar da tabbacin cewa 'yan kasa za su fara ganin canjin da su ke bukata ta fuskar tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kara hakuri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ganduje ya nemi a kara yi wa shugaban kasa uziri a lokacin da ‘yan kasa ke kara fadawa a cikin wahalhalun matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Babban malami a Arewa ya dura kan gwamnati, ya ce ita ta jawo rasa rayuka a jihohi 3

Ganduje
Ganduje ya kara ba 'yan kasa hakuri a kan wahalhalun rayuwa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Ganduje ya fadi haka ne ta cikin wata sanarwa da Mai magana da yawunsa, Edwin Olofu ya fitar don taya Kiristoci murnar bikin Kirsimetin bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abubuwa za su daidaita,” Ganduje

Jaridar The Nation ta wallafa cewa shugaban APC ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tattalin arzikin kasar zai bunkasa kuma ya daidaita nan da shekarar 2025.

Ya ce yawancin 'yan Najeriya na kokawa kan matsalolin rashin tsaro, talauci, yunwa, da kuma hauhawar farashi, abin da aka danganta da cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

Ganduje ya yaba da ayyukan Tinubu

Tsohon gwamnan Kano, kuma shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce Tinubu na aiki tukuru domin samar da romon dimokradiyya ga al’umma.

Ganduje ya ce duk da wahalhalun da manufofin Tinubu sun jefa jama’a a cikin wahala, amma gyare-gyaren da shugaban kasar ya fara sun fara kawo sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: PDP ta jefi Tinubu da kalubalen tafiya daga Abuja zuwa Legas

Tinubu ya yabi jajircewar Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 75 da haihuwa.

Shugaban ya ce Abdullahi Ganduje ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba ga jam'iyyar, tare da yi masa fatan farin ciki da ingantacciyar rayuwa a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.