"Ku Ƙara Hakuri": Sanata Ya Rabawa Mutanen Mazaɓarsa Buhunan Shinkafa 11,000

"Ku Ƙara Hakuri": Sanata Ya Rabawa Mutanen Mazaɓarsa Buhunan Shinkafa 11,000

  • Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole ya raba buhunan shinkafa 11,000 ga mutane a mazaɓarsa domin su yi shagulgulan kirismeti
  • Tsohon gwamnan ya buƙaci ƴan Najeriya su kara hakuri da halin matsin da ake ciki domin nan ba da jimawa ba komai zai daidaita
  • Oshiomhole ya kuma taya ɗaukacin ƴan Najeriya murnar kirismeti da sabuwar shekara, ya bukaci a rungumi zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo ta Arewa) ya raba buhunan shinkafa 11,000 ga al’ummar mazaɓarsa domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya watau NAN ya ruwaito cewa shinkafar ta kunshi buhuna masu nauyin kilogram 10, 25 da kuma 50kg.

Adams Oshiomhole.
Sanatan Adams Oshiomhole ya raba buhunan shinkafa 11,000 ga mutanen mazaɓarsa Hoto: Adams Oshiomhole
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an raba buhunan shinkafar ne a faɗin kananan hukumomi shida da suka haɗa mazaɓar sanatan Edo ta Arewa.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan batun jefawa mutane bama bamai a Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya tabawa mutane buhuna 11,000

Da yake jawabi yayin rabon tallafin a kananan hukumomi daban-daban ranar Laraba, Oshiomhole ya ce tallafin wani bangare ne na kokarin ragewa jama'a radaɗi.

Ya buƙaci kiristoci da sauran ƴan Najeriya sun rungumi zaman lafiya da ƙaunar juna a lokacin bukukuwa irin kirismeti.

Oshiomhole ya ce:

"Wannan shinkafa ba ta ƴan jam'iyya ba ne kaɗai, sauran jama'a kamar kanikawa, teloli da ƴan banga duk sun amfana da tallafin.
"Ba zan yi wasa da goyon bayan da kuka nuna mani ba kuma ina baku tabbacin zan ci gaba da yi maku abubuwan alheri.

Oshiomhole ya ba ƴan Najeriya haƙuri

Tsohon gwamnan wanda ya amince da cewa abubuwa sun yi tsauri, ya roki ‘yan Najeriya da su ƙara hakuri da wannan gwamnati domin komai zai daidaita.

"Na san cewa abubuwan sun yi wahala yanzu, ina rokon ku ƙara hakuri da gwamnatin APC domin nan gabaa komai zai daidaita, Najeriya za ta gyaru."

Kara karanta wannan

Babban malami a Arewa ya dura kan gwamnati, ya ce ita ta jawo rasa rayuka a jihohi 3

Sanata Oshiomhole ya taya kiristoci murnar kirsimeti da sabuwar shekara da za a yi a makon gobe.

Oshiomhole ya goyi bayan ba ɗansa muƙami

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya ce dansa ya cancanci matsayin da Monday Okpebholo ya naɗa shi.

Sanata Oshiomhole ya ce ba sau ɗaya ba, ɗansa ya nemi tsayawa takara amma yana hana shi saboda gudun abin da zai je ya dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262