Jami'an Tsaro Sun Farmaki Wajen da 'Yan Ta'adda ke Boye Boma Bomai
- ‘Yan sanda a Anambra sun kai farmaki a wata maboyar ‘yan ta’adda a kauyen Nimo da ke karamar hukumar Njikoka
- Yayin farmakin, an kwace bama-bamai da dama tare da lalata gine-ginen da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen buya
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yaba da hadin kan da ake samu tsakanin hukumomin da jama’a wajen tabbatar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta kai wani gagarumin samame a maboyar ‘yan ta’adda da ke kauyen Nimo, karamar hukumar Njikoka.
A yayin samamen, an gano wasu boma bomai guda 19, tare da lalata gine-ginen da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka.
Kakakin 'yan sanda, SP Tochukwu Ikenga ne ya wallafa labarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 25 ga Disamba, 2024 a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarar farmakin maboyar ‘yan ta’adda
SP Ikenga ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne a safiyar ranar Talata, 24 ga Disamba, tare da hadin gwiwar sojoji, jami’an NSCDC, da kungiyar tsaro ta Anambra.
Farmakin ya haifar da nasarar lalata gine-gine na wucin gadi da ke sansanin tare da raunata ‘yan ta’adda da suka tsere da munanan raunin harbin bindiga.
Kiran 'yan sanda ga asibitocin Anambra
Punch ta wallafa cewa kwamishinan ‘yan sanda na Anambra, CP Nnaghe Itam ya jinjina wa hadin kan hukumomin tsaro da goyon bayan jama’a wajen cimma nasarar.
Ya yi kira ga masu asibitoci masu zaman kansu da na gwamnati da su rika kai rahoton duk wani mutum da ya nemi magani saboda raunukan harbin bindiga ko wasu munanan raunuka.
Cigaba da farautar 'yan ta'addan Anambra
CP Itam ya jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaro ta hanyar ci gaba da gudanar da sintiri da kuma kai hare-hare a wuraren da ake zargin ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da zaman lafiya a duk fadin jihar Anambra, musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.
'Yan sanda sun kwato bindigogi 1,984 a 2024
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da rahoto a kan manyan nasarorin da ta samu a 2024.
Rundunar ta bayyana cewa ta samu nasarar kama bindigogi kimanin 1,984 a wajen miyagu tare da kama dubban masu laifi daban daban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng