Karshen Alewa: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Zamfara

Karshen Alewa: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Zamfara

  • Sojojin Najeriya tare da taimakon 'yan banga sun kashe “Al’jan,” wani dan bindiga da ya addabi mazauna yankin Tsafe
  • An ce “Al’jan” ya shiga harkar ta’addanci bayan hulda da Fulani makiyaya, inda ya taimaka wajen kai hare-hare da satar mutane
  • Mutuwar “Al’jan” ta sanya farin ciki ga mazauna Tsafe, musamman a hanyar Tsafe-Gusau da yankin Bamamu, inda yake barna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Mazauna karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun samu natsuwa bayan kashe wani hatsabibin dan bindiga mai suna “Al’jan” da ya addabi yankin.

“Al’jan,” wanda ba a gano asalin sunansa ba, ya fito daga Jamhuriyar Nijar, kuma ya zauna a Tsafe bayan aiki a matsayin direban adaidaita sahu.

Jami'an tsaro sun halaka hatsabibin dan bindiga a Zamfara
Sojoji da hadin guiwar 'yan banga sun kashe dan bindiga Al'jan a jihar Zamfara. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola Makama, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya musamman tafkin Chadi ne ya fitar da wannan rahoto a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun farmaki wajen da 'yan ta'adda ke boye boma bomai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dan bindiga Al'jan ya addabi Tsafe

Aikin adaidaita sahu ya hada Al'jan da wasu Fulani makiyaya, daga nan ya shiga harkar ta’addanci tare da kasancewa tare da wata kungiyar Hassan Bamamu.

Ya yi amfani da sanin da ya yi wa yankin Tsafe wajen taimakawa ‘yan ta’adda zuwa kai hare-hare da sace mutane a cikin yankin.

An zarge shi da kashe mutane da dama, ciki har da Anas Umar Dan Kanti, Alhaji Musa Ille da wani sojan ruwa wanda ba a ambaci sunansa ba.

Al'jan: Jami'an tsaro sun kashe dan bindiga

Ayyukan ta’addancin “Al’jan” sun zo karshe ne makonni uku da suka gabata bayan jami’an tsaro sun kashe shi da wasu ‘yan tawagarsa a wata arangama.

An ce sojojin Najeriya da hadin guiwar ‘yan banga ne suka yi kwanton bauna ga tawagar Al'jan a tsakanin Mada da Yandoton Daji da ke karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama miyagu 30,313 da bindigogi 1,984 a 2024

Mutuwar “Al’jan” ta sanya mazauna Tsafe cikin farin ciki, musamman a yankin hanyar Tsafe-Gusau, bayan an tabbatar da mutuwarsa a Bamamu.

Sojoji sun kashe shugaban 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe daya daga cikin shugabannin 'yan bindigar yankin Wase, Kachalla Saleh.

An rahoto cewa sojoji sun yi nasarar kashe Kachalla Saleh da wasu daga cikin yaransa a Kinashe, gundumar Bashar da ke Wase a jihar Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.