Ana Tsaka da Bikin Kirsimeti, Tinubu da Gwamnoni Sun Nemi Alfarmar 'Yan Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu da gwamnoni sun nemi alfarmar 'yan Najeriya yayin da ake bitain Kirsimeti a kasar da duniya baki daya
- Tinubu da gwamnoni da dama sun bukaci Kiristoci da su yi koyi da dabi'un Yesu Almasihu, ciki har da sadaukarwa da kaunar juna
- Legit Hausa ta tattaro sakonnin da wasu gwamnoni suka aikawa al'ummarsu da kuma bangarorin da suka fi ba fifiko a sakon
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, da shugabannin majalisa sun yi kira ga soyayya, zaman lafiya, da hadin kai yayin bukukuwan Kirsimeti a Najeriya.
A sakonsa na Kirsimeti, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa Kirsimeti yana nuna cikar annabta kuma alama ce ta nasarar soyayya da zaman lafiya.
Kirsimeti: Sakon Tinubu ga 'yan Najeriya
A sakonsa na Kirsimeti kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Tinubu ya fadawa 'yan Najeriya cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A wannan lokacin farin ciki na Kirsimeti, ina taya Kiristoci a Najeriya da duniya murnar zagayowar bikin haihuwar Yesu Almasihu."
Shugaba Tinubu ya ce Kirsimeti lokaci ne da kunshe da sakonni da koyarwar Almasihu ga al'ummar Kirista kuma yana nuna soyayya, zaman lafiya, da hadin kai.
Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’a ga shugabanninsu, yana mai cewa kasar na kan hanyar farfadowa da kuma samun ci gaba.
Gwamnoni sun aika sakon bikin Kirsimeti
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara ya bukaci al'umma da su yi tunani kan darussan Kirsimeti a mu’amalarsu ta yau da kullum.
Ya nemi da a gudanar da addu'o'i domin samun albarkar wannan lokaci da kuma tabbatuwar zaman lafiya a jihar Kwara da Najeriya baki daya.
Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya bukaci al’ummar jihar da su rungumi dabi’un soyayya, zaman lafiya da sadaukarwa a lokacin Kirsimeti.
Inuwa Yahaya ya kara da cewa mutane su yi tunani kan ma’anar ruhaniya na lokacin Kirsimeti tare da yin addu’a don ci gaban kasar Najeriya.
"Yesu ya koyar da zaman lafiya" - Gwamna Bala
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya bukaci Kiristoci da su yi koyi da dabi’u da koyarwar Yesu Almasihu, ciki har da nuna soyayya da tausayi ga juna.
Abdullahi Sule ya ce, yin addu’a da girmama shugabanni zai taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro da tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya tunatar da Kiristoci cewa Yesu ya koyar da zaman lafiya, gaskiya, soyayya, da tsoron Allah.
Bala Mohammed akwai bukatar mutane su yi koyi da wadannan dabi’u don samun ci gaba mai dorewa.
"Ku taimaki marasa galihu" - Gwamna Diri
Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya bukaci masu rufin asiri da su taimaka wa marasa galihu don su ma su yi bikin Kirsimeti cikin farin ciki.
Diri ya yi wannan kiran yayin taron addu’a na "Nine Lessons" na Kirsimeti na jihar Bayelsa a Yenagoa.
Shi Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya bukaci jama’ar jihar da su kara soyayya da zaman lafiya a tsakaninsu don kyautata zamantakewa.
Oyebanji kuwa ya bayyana wannan lokaci a matsayin damar yin tunani mai zurfi da addu’a don dorewar zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.
Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta shi ma ya bukaci mutane da su rungumi dabi’un soyayya, zaman lafiya, da hadin kai na wannan lokaci na Kirsimeti.
Barawo ya sace akuyar Kirsimeti a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani magidanci da ke zaune a Unguwar Azara, Gwagwalada, da ke Abuja ya kai rahoton sace akuyar Kirsimetinsa.
Magidancin mai suna Mista Solomon Isaac ya shaida cewa barawon ya haura katangar gidansa, ya sace akuyar a lokacin da shi da iyalinsa suka je coci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng