Barawo Ya Haura Katangar Gidan Wani Mutumi a Abuja, Ya Sace Akuyar Kirsimeti
- Wani barawo ya haura katangar gidan wani Mista Solomon Isaac a Abuja tare da sace akuyar da aka tirke don Kirsimeti
- Mista Isaac ya sanar da cewa ya sayi akuyar a kan N87,000 kuma an sace ne da misalin karfe 10:20 na dare lokacin yana coci
- Rundunar ‘yan sanda ta Abuja ta sanar da cewa tana ci gaba da bincike kan lamarin sace akuyar da aka yi a gidan Mista Isaac
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani da ake zargin barayo ne ya haura katangar gidan wani mutumi a Unguwar Azara, Gwagwalada, da ke Abuja ya sace akuyar Kirsimeti.
Mutumin da aka sacewa akuyar, Mista Solomon Isaac, ya bayyana cewa lamarin ya faru ranar Lahadi da misalin karfe 10:20 na dare.
An haura katanga an sace akuyar Kirsimeti
Mista Isaac ya ce ya sayi akuyar a kasuwar Gwagwalada don ya yanka a bikin Kirsimeti kuma ya daure ta a bayan gidansa, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magidancin ya ce ya tafi coci tare da iyalansa, amma lokacin da suka dawo da misalin karfe 10:23 na dare suka tarar an sace akuyar.
“Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, na kulle kofar gida lokacin da muka fita zuwa coci ranar Lahadin amma muka dawo muka ga an sace akuyar.”
- A cewar Mista Isaac.
An fara bincike domin gano akuyar
Mista Issac ya gano cewa wasu mutane sun haura katangar gidan bayan sun yanke wayar karfen tsaro da ke a saman katangar, aka dauke akuyar.
Magidancin ya ce ya sayi akuyar a kan N87,000, kuma ya kai rahoton sace ta ga masu gadi domin sa ido a kasuwanni ko wajen yanka dabbobi ko za a ganta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine, ta bukaci lokaci domin bincike kan lamarin amma ba ta yi karin bayani ba.
Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana 25 da 26 na Disamba a matsayin ranakun hutun bikin Kirsimeti ga ma'aikata.
Hakazalika, gwamnatin ta ayyana ranar 1 ga watan Janairu a matsayin ranar hutun sabuwar shekara, yayin da ta taya 'yan kasar murna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng