Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake

Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake

- 'Yan bindiga da zasu kai mutum shida sun haura katangar fadar Oba David Oyewumi inda suka yi awon gaba dashi

- Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da yammaci a Ilemeso dake garin Ekiti a jihar Ekiti

- An gano cewa wannan yankin yana daya daga cikin yankunan Oye da aka fi satar jama'a tare da karbar kudin fansa

Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a gano ko su waye ba a yammacin ranar Alhamis sun tsinkayi fadar Obadu na Ilemeso dake Ekiti a jihar Ekiti.

Sun sace basaraken mai suna Oba David Oyewumi kuma sun yi awon gaba dashi zuwa inda har yanzu ba a gano ba, Leadership ta ruwaito.

Ilemeso na daya daga cikin yankunan karamar hukumar Oye dake jihar wacce ake yawaita satar jama'a domin karbar kudin fansa a watanni kadan din nan.

'Yan bindigan da zasu kai shida, sun taru ne inda suka tsallake katangar fadar basaraken sannan suka dinga harbe-harbe domin tsoratar da jama'a.

KU KARANTA: Jaruma mai kayanmata ta wallafa wasu bidiyo na taya ma'aikatanta 4 murnar aurensu

Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake
Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake
Asali: Original

KU KARANTA: Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce rundunarta ta Operation Lafiya Dole ce ke rike da garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

A ranar Talata ne aka tabbatar da cewa 'yan ta'addan Boko Haran sun kai farmaki garin. Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a garin Abuja.

Yerima ya ce rahotannin da wasu bangare na kafafen yada labarai ke bayyana na cewa 'yan ta'adda sunkwace garin Damasak duk babu gaskiya a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng