Kotun Shari'ar Musulunci: Gwamna Ya Fito Ya Fayyace Lamarin, Ya Fadi Matakin Ɗauka
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi martani kan rikita-rikitar da ake yi kan shirin kafa kotunan Shari'ar Musulunci
- Gwamnan ya tabbatar da cewa zai tsaya tsayin daka wajen ganin an bi doka da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya
- Mai girma Makinde ya bayyana cewa a kowane shiri, ciki har da kafa kotun Shari'a, dole ne ya kasance bisa ka'idar doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya yi magana kan rigimar da ta taso kan shirin kafa kotunan Shari'ar Musulunci a jihar.
Gwamnan ya ce kan batun kafa kotun Shari'a a birnin Oyo zai tabbatar da cewa ya kare doka da kundin tsarin mulki.
Gwamna ya magantu kan kafa kotunan Musulunci
A cikin wata hira da Tribune ta bibiya, Makinde ya ce mutane na iya yin wasu shirye-shirye, amma dole ne su tsaya cikin ka'idar doka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya jaddada cewa duk wani shiri da ba ya cikin doka zai fuskanci mataki mai tsanani domin tabbatar da bin dokoki.
"Game da kafa kotun Shari'a a Oyo, idan shirin yana cikin doka, babu matsala, amma idan ba haka ba, zan dauki mataki."
- Seyi Makinde
Kotun Musulunci: Gargadin da gwamna ya yi
Makinde ya kuma kara da cewa ya rantse zai tsaya tsayin daka wajen kare doka da kundin tsarin mulkin Najeriya yadda ya kamata.
Gwamnan ya yi gargadi cewa ba zai bari a karya doka ba, domin zai tabbatar da cewa an yi komai bisa tsarin da ya dace, cewar The Guardian.
Shirin kafa kotun shari'ar ya jawo surutu
Wannan batu ya jawo hayaniya a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra'ayinsu daban-daban.
Wasu na ganin kafa kotun Shari’a a jihar ya dace, yayin da wasu ke ganin hakan zai iya sabawa tsarin mulki.
Za a bude kotun Shari'ar Musulunci a Oyo
Kun ji cewa wata kungiyar Musulmai ta shirya kaddamar da sabuwar kotun shari’ar Musulunci a Oyo a ranar 11 ga watan Janairun 2025.
Wannan shiri ya jawo martani daga wasu da ke ganin kafa kotun zai kawo matsaloli ga walwala da 'yancin mutanen Kudancin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng