"Lokacin Farin Ciki na Tafe," Uwar Gidar Shugaba Tinubu Ta Aika Sako ga Ƴan Najeriya

"Lokacin Farin Ciki na Tafe," Uwar Gidar Shugaba Tinubu Ta Aika Sako ga Ƴan Najeriya

  • Uwar gidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta tabbatarwa ƴan Najeriya cewa ranakun farin ciki na nan tafe a shekarar 2025
  • Oluremi ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar domin taya ƴan Najeriya murnar zagayowar kirismeti da sabuwar shekara
  • Ta ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen kawo sauye-sauyen da za su amfani kowane ɗan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci ‘yan Najeriya da su fara shirye-shiryen shiga sabuwar shekara watau 2025.

Matar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ce ranakun farin ciki da alheri suna nan tafe a sabuwar shekarar da ke dab da shigowa.

Oluremi Tinubu.
Uwar gidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta taƴa ƴan Najeriya murnar kirsimeti Hoto: Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Uwargidar Tinubu ta taya ƴan Najeriya murna

Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne a sakon taya ƴan Najeriya murnar zagayowar kirismetin bana 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Ku yi mani addu'a': Tinubu ya roki yan kasa bayan jawabinsa da ya fusata al'umma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Tinubu ta nuna matukar jin dadin ta game da “goyon baya da hakuri da ake ba mu yayin da muke kokarin gina ingantacciyar Najeriya.”

Ta kuma bai wa ƴan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta ɓullo da sauye-sauyen masu kyau da za su amfani al'umma.

Oluremi Tinubu ta ce farin ciki na tafe

“Ina tabbatar muku da cewa a gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, mun himmatu wajen kawo sauyi mai kyau da zai amfani kowane dan Najeriya. Yawanci sun fara haifar da ɗa mai ido."
"Yayin da muke bankwana da wannan shekarar, mu sa a ranmu cewa kyawawan ranaku na farin ciki suna nan tafe, mu nuna wa junanmu goyon baya, mu haɗa kai, mu manta da banbancin da ke tsakaninmu."
"Ina taya gaba ɗaya ƴan Najeriya murnar Kirismeti da sabuwar shekarar 2025 cikin farin ciki, ƙauna, zaman lafiya da kwanciyar hankali."

- Sanata Oluremi Tinubu.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Tinubu ta gaza," Jigon APC ya amince sun ba ƴan Najeriya kunya

Bola Tinubu ya roki a masa addu'a

Kun ji labari cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ƴan Najeriya sanya shi da sauran shugabanni a cikin addu'o'insu.

Bola Tinubu ya ce addu'a tana da matukar muhimmanci ga shugabanni domin su samu nasarar kawo ci gaba mao ɗorewa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262