Ajali Ya Yi: Wata Tirela Ta Murkushe Mai Adaidaita Sahu, Bayin Allah Sun Rasu

Ajali Ya Yi: Wata Tirela Ta Murkushe Mai Adaidaita Sahu, Bayin Allah Sun Rasu

  • Wata tirela ta markade mai Keke Napep a Jos da ke jihar Filato, mutum uku sun riga mu gidan gaskiya ranar Litinin da yamma
  • Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar hatsarin, ta ce yanzu haka mutum huɗu na kwance suna jinya a asibiti
  • Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya auku ne lokacin da tirelar ta ci karo da mai adaidaita sahun a titin Farin Gida da ke Jos ta Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, jihar Plateau - Wani ibtila'i ya afku a jihar Filato da yammacin ranar Litinin, inda mutum uku suka mutu, wasu huɗu suka samu raunuka a hatsarin mota.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Farin Gada a Jos ta Arewa lokacin da wata tirela ta yi karo da adaidaita sahu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace matafiya kusan 20, sun nemi a biya sama da Naira miliyan 500

Taswirar jihar Filato.
Mutum 3 sun mutu yayin da tirela ta take Keke Napep a Jos Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tirela ta yi taho mu gama da adaidaita sahu

Kakakin hukumar kiyaye haɗurra (FRSC), Peter Yakubu da shugaban ƙungiyar agaji ta Red Cross, Nura Ussaini Magaji sun tabbatar da afkuwar hatsarin ga Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa wasu daga cikin gawarwakin an markaɗe su ta yadda ba za a iya gane waye ba ballantana a nemi ƴan uwansa.

A cewarsu, hatsarin ya afku ne a ranar 23 ga watan Disamba, 2024 a kusa da dakin kwanan dalibai na jami'ar Jos da ke jihar Filato a Arewa ta Tsakiya.

Hukumar FRSC ta faɗi waɗanda suka mutu

Kakakin hukumar FRSC na jihar Filato, Peter Yakubu ya ce mutum uku sun mutu, yayin da wasu mutum huɗu suka samu raunuka daban-daban.

"Hatsarin ya afku ne a ranar 23 ga watan Disamba a kusa da dakin kwanan dalibai na jami'ar Jos. Ababen hawa biyu ne hatsarin ya rutsa da su, tirela da babur mai ƙafa uku.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da jirgin kasa ya murkushe wata mota a Legas, mutane sun magantu

“Mutane uku ne suka mutu yayin da wasu hudu kuma suka samu raunuka daban-daban a hadarin."

- Peter Yakubu.

Tankar mai ta kama da wuta a Ekiti

A wani labarin, kun ji cewa an shiga fargaba da wata tankar dakon mai ta faɗi a gefen titi kuma wuta ta kama a jihar Ekiti.

Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa reshen jihar Ekiti ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce babu wanda ya rasa ransa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262