Gwamna Ya Rasa Kwamishinoni a Ofis yayin Ziyarar ba Zata, Ya yi Gargadi

Gwamna Ya Rasa Kwamishinoni a Ofis yayin Ziyarar ba Zata, Ya yi Gargadi

  • Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya gargadi kwamishinoni da manyan sakatarori kan kin zuwa aiki a kan lokaci
  • Sanata Bala Mohammed ya ce hukumomin gwamnati za su dauki matakan ladabtarwa kan duk wanda aka samu da sakaci
  • Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ziyarar ba zata da ya kai sakatariyar Bauchi domin ganewa idonsa yadda ayyuka ke tafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya bukaci ma’aikatan gwamnati da suka hada da kwamishinoni da manyan sakatarori su kara jajircewa.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne yayin wata ziyarar ba zata da ya kai Sakatariyar Abubakar Umar da ke Bauchi a ranar Litinin.

Bala Muhammad
Gwamna Bala Muhammad ya kai ziyarar ba zata ma'aikata. Hoto: Lawal Mu'azu Bauchi
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Bala Mohammed a harkokin sadarwa, Lawal Mu'azu Bauchi ne ya wallafa yadda ziyarar ba zatan ta gudana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rage matsalar rashin aikin yi, ya dauki ma'aikata kusan 500

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ziyarar, gwamnan ya duba ofisoshi tare da nuna damuwa kan rashin halartar wasu manyan jami'an gwamnati wajen aiki.

Gwamna Bala ya gargadi ma'aikatan Bauchi

A yayin da ya gudanar da sallar La'asar tare da ma’aikata a masallacin ma’aikatar, Gwamna Bala Mohammed ya jaddada muhimmancin adalci da kishin kasa ga ma’aikatan gwamnati.

Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci sakaci ko rashin ladabi wajen gudanar da aiki ba, ya bukaci ma’aikata su rika zuwa aiki a kan lokaci domin kara inganta ayyukansu.

Magana kan aikin dakin taron sakatariyar

Yayin da ya ziyarci ginin dakin taro na ma’aikatar, gwamnan ya bayyana takaicinsa kan yadda aikin ke tafiyar hawainiya duk da yawan kudin da aka kashe a kansa.

Ya bukaci wadanda ke kula da aikin su kara himma domin ganin an kammala shi cikin lokaci tare da inganta shi.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya ziyarci mutanen da aka ceto a hannun 'yan bindiga, ya ba da tallafi

Za a ladabtar da ma'aikata a Bauchi

Da yake magana da manema labarai bayan kammala ziyarar, Gwamna Bala ya jaddada cewa gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan duk wanda bai zuwa aiki a kan lokaci ba.

Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an dauki matakan ladabtarwa ga duk wanda aka samu da laifi domin inganta aikin gwamnati a jihar Bauchi.

Ana gina makarantar Dahiru Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta fara gina katafairiyar makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa makarantar za ta rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta kuma ita ce irinta ta farko a Arewa maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng