Musulmai Za Su Bude Kotun Shari'ar Musulunci a Najeriya, Cacar Baki Ta Barke a Kudu

Musulmai Za Su Bude Kotun Shari'ar Musulunci a Najeriya, Cacar Baki Ta Barke a Kudu

  • Wata kungiyar Musulmai ta shirya kaddamar da sabuwar kotun shari’ar Musulunci a Oyo a ranar 11 ga watan Janairun 2025
  • Wannan shiri ya jawo martani daga wasu da ke ganin kafa kotun zai kawo matsaloli ga walwala da 'yancin mutanen Kudu
  • Wasu sun yi kira da a dakatar da bude kotun shari’ar Musuluncin saboda hadarin rabuwar kawuna a tsakanin mabiya addinai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Wata kungiyar Musulunci a karkashin Majalisar Koli ta Shari’ah a Najeriya, ta shirya kaddamar da wata kotun shari’ar Musulunci a jihar Oyo.

A wata takarda da ta yadu a shafukan sada zumunta a ranar Talata, kungiyar ta gayyaci kowa da kowa zuwa kaddamar da kotun a ranar 11 ga Janairu, 2025.

Cacar baki ta barke a soshiyal midiya yayin da ake shirin bude kotun musulunci a Oyo
Bude kotun shari'ar Musulunci a Oyo ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Za a bude kotun Musulunci a jihar Oyo

Kara karanta wannan

Yankin Yarbawa sun magantu kan yiwuwar kafa Shari'ar Musulunci, sun fadi matsayarsu

Takardar ta lissafa wasu manyan baki a taron, ciki har da Bashorun na Oyo, Alhaji Yusuf Olayinka, da wasu manyan shugabannin Musulunci, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin takardar sanarwar, an ga cewa Aare na Musulmin Oyo, Alhaji Tajudeen Abdul-Hameed Kamorise ne babban mai masaukin baki, yayin da taron zai fara da karfe 10 na safiya.

Sanarwar ta ce za a gudanar da taron ne a cibiyar al'ummar Musulmi da ke kan titin makarantar Oba Adeyemi, yankin Mabolaje, karamar hukumar Ibadan ta Arewa.

'Yan Kudu na adawa da bude kotun

Sai dai kuma kaddamar da kotun Musuluncin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke cewa Kudu maso Yamma ba wurin da Musulmai ke rinjaye kamar Arewa ba ne.

Wani mai amfani da X, @OurFavOnlineDoc, ya ce shari’ar Musulunci na iya zama barazana ga rayuwa da walwalar mutane, musamman ga marasa galihu da matalauta.

Wani mai amfani da dandalin X, @ILE_AJISEFA, ya yi kira da a yi watsi da dokar shari’ar Musulunci a Kudu maso Yamma saboda matsalolin da za ta haifar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ritsa 'yan ta'adda a wajen da suke tsafi, an kashe miyagu da dama

Wasu suna ganin kafa kotun shari'ar Musulunci za ta haifar da matsalar kabilanci da addini, tare da rage walwala da yanci a yankin.

Kotun Musulunci: Yarbawa sun gargadi gwamnati

A wani labarin, mun ruwaito cewa matasan yankin Yarbawa sun fito fili sun nuna adawa da shirin kafa kotun shari'ar Musulunci a jihar Oyo.

Shugabannin matasan sun ce za su yi duk mai yiwuwa domin kare yankin Kudu maso Yamma daga yunkurin kafa kotun da zai iya kawo rikici.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.