IPMAN Ta Fadi Dalilin Kin Cika Alkawarin Fara Sayar da Litar Fetur a kan N935
- Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta tabbatar da cewa har yanzu ba ta fara sayar da fetur mai rahusa ba
- Shugaban kungiyar, shiyyar Arewa maso Yamma, Salisu Ten-Ten ya ce akwai abin da ya hana su fara aiwatar da haka
- Jinkirin na zuwa bayan masu ruwa da tsaki a bangaren fetur sun sa wa jama'a rai da samun saukin tsadar mai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kungiyar dilalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta gaza cika alkawarin da ta yi na fara sayar da kowace litar fetur a kan farashi mai rangwame.
Kamfanin mai na kasa (NNPCL) da Matatar Dangote sun rage farashin mai da su ke sayar wa 'yan kasuwa domin a sayar wa talaka da sauki.
BBC Hausa ta ruwaito cewa amma an samu tsaiko a wajen fara cika alkawarin da 'yan kungiyar IPMAN su ka dauka tun tuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin IPMAN na jinkirta saukaka farashin fetur
Shugaban dillalan na shiyyar Arewa maso Yamma, Salisu Ten-Ten ya bayyana cewa ba yanzu za su fara sayar da man fetur a kan sabon farashin N935 ba.
Salisu Ten-Ten ya ce 'yan kasa za su fara sayen fetur a farashin N935 ne idan tsofaffin kaya da su ka sayo sun kare tas, amma bai fadi yaushe ne ba.
IPMAN ta amince da rage farashin fetur
A karin bayani da ya yi wa majiyar Legit a Kano, Sakataren kudi na IPMAN , Musa Yahaya Mai Kifi ya ce batun fara sayar da man Dangote a kan N935 na nan. Ya ce:
"Akwai tattaunawa da ake yi tsakanin MRS, ma'ana Dangote din ke nan da kungiyar dillalan man fetur cewa ana son su rika dauko man a kan N935, a zo kuma a sayar da shi a kan N930."
"Amma za a biya kudin dako, sannan za a biya wanda ya saida a gidan mansa kudin ribarsa da kuma wahalhalun gidan mansa. To amma gaskiya har yanzu ba a gama tattaunawa ba.
"Domin maganar da ake yi, harkar biyan kudin dako din, har yanzu ba a samu matsaya a kanta ba, saboda a halin da ma mu ke ciki har yanzu, akwai kudadenmu a hannun gwamnatin tarayya ko kuma a hannun NMDPRA."
IPMAN ta shiga yarjejeniya da Dangote
A baya, kun ji cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta tabbatar da cewa ta shiga yarjejeniya da matatar Ɗangote domin a fara sayar da litar fetur da sauki.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Maigandi Haruna ne ya tabbatar da haka, inda ya kara da cewa za a fara sayar da fetur a kan N935 kowace lita, sai dai hakan ba ta tabbata ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng