Yankin Yarbawa Sun Magantu kan Yiwuwar Kafa Shari'ar Musulunci, Sun Fadi Matsayarsu

Yankin Yarbawa Sun Magantu kan Yiwuwar Kafa Shari'ar Musulunci, Sun Fadi Matsayarsu

  • Ƙungiyar matasan Yarbawa ta yi fatali da shirin kafa kotunan Shari’ar Musulunci a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Shugabannin ƙungiyar sun ce za su kare yankin su daga duk wani yunkurin da zai kawo rikici, ciki har da kafa dokokin da ba na al'adunsu ba
  • Sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya cewa duk wani yunƙuri na kawo rarrabuwar kawuna a ƙasar Yarbawa zai gamu da matuƙar adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Wata ƙungiya mai suna 'Yoruba Youth Nation' ta yi tir da shirin kafa kotunan Shari’ar Musulunci.

Ƙungiyar Yarbawan ta ce ba za ta lamunci kokarin kafa Shari’ar Musulunci ba a yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Kungiyar Yarbawa ta yi fatali da shirin kafa shari'ar Musulunci
Kungiyar matasan Yarbawa ta ce ba za ta amince da shirin kafa shari'ar Musulunci ba. Hoto: Legit.
Asali: Original

Kungiyar Yarbawa ta magantu kan shari'ar Musulunci

A wata sanarwa da shugabanninta, Ayodele Ologunloluwa da Oyegunle Omotoyole, suka fitar, ƙungiyar ta ce za su kare ƙasar su daga duk wani yunƙuri na kawo rikici, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ritsa 'yan ta'adda a wajen da suke tsafi, an kashe miyagu da dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta biyo bayan labarin cewa Majalisar Kolin Shari’a ta Najeriya reshen jihar Oyo za ta kafa kotun Shari’ar Musulunci a garin Oyo.

An shirya gudanar da bikin ƙaddamarwar a ranar 11 ga Janairun 2025, a Cibiyar Musulunci ta Al’umma, kusa da makarantar Oba Adeyemi.

Sai dai, matasan sun ce wannan shirin abin dariya ne, suna mai cewa za su tashi tsaye domin kawo ƙarshen duk wani yunƙuri irin wannan.

Yarbawa sun nuna damuwa kan shari'ar Musulunci

“Ba za mu amince a kafa dokar Shari’a ko kotunan Shari’ar Musulunci ba a ƙasar Yarbawa.”
“Al’adar Yarbawa ta bambanta da na wasu al’ummomi, kuma duk wani yunƙuri na kawo dokokin da suka saba al'adunmu za mu yi tawaye.”
“Shari’a ba ta dace da al’adunmu, dabi’unmu, ko salon rayuwarmu ba, ba za mu bari wani ya kawo hargitsi a yankinmu da sunan addini ba.”

- Cewar sanarwar

An daure tsohon alkalin Kotun shari'ar Musulunci

Kara karanta wannan

Yunwa: PDP ta alakanta turmutsitsin da ya hallaka jama'a da manufofin Tinubu

Kun ji cewa wani tsohon alkalin kotun shari'ar Musulunci ya shiga hannu kan zargin cin zarafin matar aure da ta ke makauniya.

An gurfanar da wanda ake zargin, Mahmud Shehu a gaban kotun majistare da ke Zaria a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.