Kano: Bayan Kwanaki a NNPP, Hon. Danbatta Ya Bar Kwankwasiyya zuwa APC

Kano: Bayan Kwanaki a NNPP, Hon. Danbatta Ya Bar Kwankwasiyya zuwa APC

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya ya karɓi Alhaji Sani Garka Dambatta a matsayin sabon ɗan jam’iyyar APC
  • Alhaji Garka, wanda ya yi fice a siyasar Kano, ya bar NNPP zuwa APC domin cigaba da bayar da gudunmawa wajen cigaba
  • Ana kallon sauya shekar Alhaji Sani Garka Dambatta a matsayin karin karfi ga jam'iyyar APC mai fama da adawa a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya karbi fitaccen ɗan siyasa a jihar Kano, Alhaji Sani Garka Dambatta zuwa APC.

Alhaji Garka Danbatta ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC da niyyar bada gudunmawa ga ci gaban siyasa da tattalin arzikin jihar Kano.

Barau
HOn. Danbatta ya koma APC. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya lissafa ayyukan alheri da Tinubu ya shiryawa jihar Kano da Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An hango wasu 'yan APC yayin da aka sauyawa Alhaji Garka Danbatta jar hula, alamar da ke nuna fitarsa a tafiyar Kwankwasiyya da NNPP.

Gudunmawar Sani Garka a siyasar Kano

Sanata Barau ya ce Alhaji Sani Garka Dambatta ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasar Kano masu tasiri, tare da taka rawar gani wajen ƙarfafa cigaban jihar.

A yayin taron karɓar sa, Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya yaba da gudunmawar Alhaji Garka ga jihar Kano, yana mai cewa dawowar sa cikin APC abin farin ciki ne.

Ana ganin Hon. Garka Danbatta ya yanke shawarar shiga APC ne domin ya haɗa hannu da shugabanni wajen tabbatar da cigaba mai ɗorewa a Kano da Najeriya baki ɗaya.

Da na yi batan kai na shiga dawa sai Allah ya shirye ni na dawo gida wajen sarkin kudi, sarkin Turanci, sarkin kyautatawa 'yan jam'iyya."

Kara karanta wannan

Shugaban APC, Ganduje ya bayyana shirinsu a kan 'yan Najeriya

Na bar jam'iyyar NNPP mai kayan gwari, na dawo jam'iyyar APC."

- Hon. Garka Danbatta

Tarin 'yan NNPP sun koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa jagora a APC a Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya karbi tarin 'yan NNPP da suka fice daga tafiyar Kwankwasiyya.

Legit ta rahoto cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan ya karbi tarin mutanen jam'iyyar NNPP ne ne a birnin tarayya Abuja zuwa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng