"Aikinmu Ya na Kyau:" Tinubu Ya Fadi Kokarin da Gwamnatinsa Tayi wa Arewacin Najeriya

"Aikinmu Ya na Kyau:" Tinubu Ya Fadi Kokarin da Gwamnatinsa Tayi wa Arewacin Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana jin dadinsa saboda karuwar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya a mulkinsa
  • Tinubu ya bayyana haka ne a hirarsa ta farko da manema labarai bayan ya karbi rantsuwar aiki a watan Mayu, 2023
  • Shugaban ya ce duk da nasarorin da jami'an tsaro su ke samu, akwai rawar da 'yan Najeriya za su taka don hakan ya dore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Shugaba kasa, Bola Tinubu ya bayyana jin dadin yadda gwamantinsa ke samun nasara a wajen yaki da rashin tsaro da ya addabi jama’a, musamman na Arewa.

A hirar sa ta farko da manema labarai tun bayan ya zama shugaban kasa, Tinubu ya bayar da tabbacin cewa an samu saukin matsalolin tsaron da ya tarar.

Kara karanta wannan

Radadin cire tallafi: Tinubu ya fadi yadda abokinsa ya gagara rike manyan motoci 5

Tinubu
Shugaban kasa ya yabi jami'an tsaro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta wallafa cewa shugaban ya bayyana wuraren da aka fi samun saukin matsalolin tsaro saboda ingancin ayyukan jami’an tsaron kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya jinjinawa ci gaban tsaro

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shuaaban kasa, Bola Tinubu ya jinjinawa shugabanni da sauran jami’an tsaro saboda fatattakar matsalolin tsaron da ake da su.

Tinubu ya kara da cewa an samu karuwar tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa idan aka kwatanta da gwamnatin baya, wacce Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Tinubu ya fadi inda tsaro ya inganta

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce yanzu 'yan Najeriya su na iya tafiye-tafiye ba tare da irin kalubalen tsaro da aka rika gani a baya ba.

Tinubu ya wanda ya yi lissafin da samun saukin matsalar rashin tsaro a titin Kaduna zuwa Kafanchan ya ce;

“Yanzu za ku iya yin tafiye-tafiye. A da, hakan ba zai yiwu ba. Abu guda kacal zai iya dagula al’amuran tsaron yanki, amma ba za mu yi watsi da kokarin sojojinmu ba saboda daidaikun hare-hare da ake kai wa.”

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Amnesty ta yi zargin ana son 'karasa' matashin da 'yan sanda suka jefawa gurneti

Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su kasance masu taka tsantsan, yana mai jaddada cewa makiya cikin gida da wajen kasa suna bibiyar cigaban da ake samu.

Shugaba Tinubu ya magantu kan hauhawar farashi

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya sanar da 'yan kasa cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin sauko da farashin kayayyaki da su ka yi tashin gwauron zabo.

Amma ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta dauki shawarar kayyade farashin kayayyaki ba, inda ya ce matakin da zai dauka zai sa farashin ya sauko da kansa ba tare da katsalandan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.