Abin da Kungiyar Musulunci Ta Fadawa Wike kan Tsige Ɗan Arewa daga Shugabancin FCDA

Abin da Kungiyar Musulunci Ta Fadawa Wike kan Tsige Ɗan Arewa daga Shugabancin FCDA

  • MURIC ta bukaci Nyesom Wike ya dawo da Injiniya Shehu Ahmad Hadi kan mukaminsa na shugaban hukumar raya Abuja ta FCDA
  • Kungiyar Musuluncin ta ce rashin bayyana dalilin dakatar da Hadi ya nuna alamun rashin bin ka’ida da rashin adalci daga Wike
  • MURIC ta ce akwai rashin gaskiya a wasu matakan ministan Abuja, ciki har da rushe gidaje da ba mutanen yankinsa mukamai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta bukaci ministan Abuja, Nyesom Wike da ya dawo da Injiniya Shehu Ahmad Hadi a mukamin shugaban FCDA.

MURIC ta bukaci Nyesom Wike ya fito fili ya bayyana dalilin dakatarwar da ya yi wa Hadi idan ba zai iya mayar da shi kan mukaminsa ba.

Kungiyar MURIC ta yi magana kan matakin Wike na tsige Hadi daga shugaban FCDA
Kungiyar Musulunci ta bukaci Wike ya daow da Hadi kan shugabancin FCDA. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan a wata sanarwa, yana mai jaddada cewa Wike bai fadi dalilin dakatar da Hadi ba, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Likitoci sun sanya ranar tsunduma yajin aiki, sun yi wa ministan Tinubu barazana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC ta bukaci a dawo da Injiniya Hadi

Ya tuna cewa Wike ya dakatar da Injiniya Hadi a matsayin shugaban FCDA tun ranar 14 ga Nuwamba, 2024, ba tare da wani dalili ba.

MURIC ta ce Injiniya Hadi mutumin kirki ne wanda ya rike mukamin kwamishinan ayyuka a jihar Gombe, kuma bai taba samun matsala a aikin gwamnati ba.

Kungiyar ta kara da cewa rashin bayyana dalilin dakatarwa na iya nuna cewa ba a bi ka’ida ba, musamman ma ganin cewa ba a sanar da dalilin ba har yanzu.

Kungiyar MURIC ta zargi Wike da rashin adalci

Farfesa Ishaq Akintola ya sanar da cewa:

"Idan ana so a tabbatar da gaskiya, to ya kamata a fadawa Injiniya Shehu Hadi dalilin dakatar da shi kuma a ba shi damar kare kansa."

Farfesa Akintola ya ce wasu daga cikin matakan Wike suna kama da na mulkin mallaka, musamman wajen rushe gidajen mutane da nada mutanen yankinsa mukamai.

Kara karanta wannan

Wike ya shirya tatsar N30bn daga masu filaye a Abuja, an gindaya wa'adin biyan kudi

MURIC ta ce bai dace minsitan Abuja ya yi wa Injiniya Shehu Ahmad Hadi, wanda ya taimaka wajen nasarar shugaba Tinubu, irin wannan wulakanci ba.

Abin da ya sa Wike ya sauke Hadi

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu majiyoyi daga hukumar raya Abuja sun bayyana dalilin Nyesom Wike na korar Injiniya Shehu Hadi daga shugaban FCDA.

Majiyoyin sun shaida cewa Injiniya Hadi ya kasance yana bayyana ra'ayinsa kan ayyuka da kwangilolin hukumar, wanda hakan ya saba da ra'ayin ministan Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.