Radadin Cire Tallafi: Tinubu Ya Fadi Yadda Abokinsa Ya Gagara Rike Manyan Motoci 5
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bada labarin yadda cire tallafin man fetur ya shafi wani abokinsa a Najeriya
- Tinubu ya ce abokinsa ya daina amfani da motocinsa kirar Rolls-Royce biyar zuwa 'Honda' saboda tsadar man fetur
- Tinubu ya bayyana labarin ne domin jaddada illolin cire tallafin mai da bukatar ‘yan Najeriya su saba da sauyin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba yan Najeriya shawara kan sabawa da sauyin tattalin arziki a Najeriya.
Tinubu ya ba da labarin wani abokinsa wanda ya taba mallakar motoci kirar Rolls-Royce guda biyar, amma yanzu ya koma amfani da Honda.
Tinubu ya ba da shawara kan cire tallafi
Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin hira da yan jaridu a Lagos wanda hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa bidiyon a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin hirar, Tinubu ya ba da misali ne don bayyana yadda cire tallafin mai ya shafi tattalin arziki da halin rayuwar mutane a Najeriya.
A cewarsa, abokin nasa ya ce tsadar farashin mai ce ta sa ya kasa kula da motocinsa guda biyar, don haka ya koma amfani da Honda.
'Yadda cire tallafi ya shafi abokina' - Tinubu
“Abokina yana da kusan Rolls-Royce guda biyar; a kwanakin baya na gan shi cikin Honda, ya ce wannan shi ne halin da ka saka ni a ciki, sai na ce ban sa ka ba, ya ce saboda farashin mai, ba zai iya kula da irin motocin har guda biyar ba."
- Bola Tinubu
Tinubu ya nuna cewa wannan lamari yana da alaka da burin gwamnatinsa na gyaran tattalin arziki da kuma rage dogaro da tallafin mai.
Tinubu ya shawarci yan Najeriya kan tsadar wuta
A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya ba ‘yan Najeriya shawara kan yadda za su koyi amfani da wutar lantarki.
Tinubu ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kara farashi, amma gwamnati za ta yi kokarin samar da kayayyaki masu araha.
Shugaban ya shawarci yan Najeriya su riƙa kashe wutar lantarki musamman a lokacin da ba a amfani da ita domin samun sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng