Zanga Zanga: Amnesty Ta Yi Zargin Ana Son 'Karasa' Matashin da 'Yan Sanda Suka Jefawa Gurneti

Zanga Zanga: Amnesty Ta Yi Zargin Ana Son 'Karasa' Matashin da 'Yan Sanda Suka Jefawa Gurneti

  • Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty International ta yi zargin wasu da 'sace' fayil din matashi, Muhammad Liman
  • Matashin ya na daga cikin mutane hudu da jami'an tsaro su ka jefa wa gurneti lokacin da su ke bakin aiki a wani gidan mai a Borno
  • Shugaban kungiyar na kasa, Isa Sanusi ya shaida wa Legit cewa fayil din matashin ya bace ko sama ko kasa makonni uku baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Kungiyar Amnesty Int'l ta bayyana damuwa matuka kan bacewar fayil din wani bawan Allah Muhammed Liman daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Matashin ya na daga cikin mutane hudu da jami’an tsaro su ka jefa wa gurneti a ranar farko ta gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa a 1 Agusta, 2024 a Borno.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Tinubu ya fadi shirin gwamnatinsa a kan rage tsadar kayayyaki

Borno
Amnesty ta yi fargabar ana kokarin illata matashi a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Amnesty Int'l ta wallafa a shafinta na Facebook cewa akwai fargabar an shirya makarkashiya ga matashin da jami’an tsaron Najeriya su ka nakasa ba tare da aikata laifin komai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amnesty Int'l ta koka da jikkata matashi

A zantawar shugaban Najeriya na Amnesty International, Isa Sanusi da Legit, ya bayyana cewa Muhammad Liman na tsaka da aiki a da abokansa a lokacin da aka jefa masu gurneti.

Ya kara da cewa mutum uku daga cikin matasan sun rasu nan take, yayin da shi kadai da yar ayu kuma ya samu matsalar laka, ba ya iya motsa jikinsa ko kadan.

Sanusi Isa ya kara da cewa;

“Abokan aikinsa na gidan man A.A Kime da ke Balori junction a Maiduguri su uku sun mutu, amma shi Allah Ya masa tsawon rai amma kuma ya samu tabuwa a gadon bayansa. Lakarsa ta baya ta tabu, don haka baya iya motsa jikinsa.”

Kara karanta wannan

Zaratan 'yan Najeriya 50 za su je Fatakwal domin gano gaskiyar a matatar NNPCL

Borno: Amnesty za ta binciki batan fayil

Kungiyar Amnesty Int’l ta bayyana fargabar cewa akwai wata makarkashiya da aka shirya a kan matashin da ke kwance rai a hannun Allah.

Ya ce;

“Makonni uku da suka gabatam fayil dinsa na asibiti sama ko kasa, ba a gani ba. Don haka shi yasa mu ke da damuwa a kan akwai wani abu da ke faruwa da ya kamata mutane su sani. Kamata ya yi asibitin nan duk inda ya ke su nemo shi.”

'Yan sanda sun soki rahoton Amnesty

A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta yi tir da rahoton da kungiyar fafutukar kare hakkin bil adama ta duniya, Amnesty International a kan masu zanga-zanga.

A rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar da rahoton da ke zargin jami'an tsaro da kashe mutaene 24 a fadin Najeriya a zanga-zangar kwanaki 10 da aka yi a watan Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.