Neman Aiki, Rabon Abinci da Sauran Lokutan da 'Yan Najeriya Suka Mutu a wajen Turmutsutsi
FCT, Abuja - A cikin shekarun da suka gabata, ƴan Najeriya da dama sun yi asarar rayukansu cikin turmutsutsi da ya ritsa da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Rashin tsari mai kyau, rashin haƙuri, ƙosawa da sauran abubuwa sun ba da gudummawa wajen aukuwar waɗannan bala'o'in da za a iya hana aukuwarsu a manyan tarurruka.
Ƴan Najeriya na rasuwa a wajen turmutsuti
An yi asarar rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba sakamakon turmutsutsi, kama daga tarurrukan coci zuwa rabon abinci da aikin ɗaukar ma'aikata, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rarraba abinci shine babban abin da ke haifar da mafi yawan turmutsutsin da ake samu.
Na baya-bayan nai dai sune waɗanda suka auku a birnin tarayya Abuja da jihar Anambra inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Ga wasu fitattun turmutsutin da suka faru a baya da suka yi sanadiyyar rasa rayuka.
1. Rabon abinci a bikin Sallah a Kwara
A ranar 16 ga watan Oktoba, 2013, kimanin mutane 20 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a wani turmutsitsin da aka yi na bikin Sallah a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a yayin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ke gudanar da aikin raba kayan abinci na shekara-shekara.
2. Turmutsutsi a cocin Anambra
A ranar 2 ga watan Nuwamba, 2013, aƙalla mutane 25 ne suka mutu, wasu 200 kuma suka samu raunuka a wani turmutsitsin da ya faru a cocin Holy Ghost Adoration Ministry da ke Uke, Idemili ta Kudu a jihar Anambra.
An tattake masu ibada da yawa a lokacin da mutane suka nemi tsira da rayukansu a harabar cocin.
An ba da rahoton cewa, wasu masu ibada sun yi ƙaryar tashin gobara a lokacin da ake gudanar da taron cocin, lamarin da ya sa mutane suka yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.
3. Ɗaukar aikin hukumar NIS
Yawancin ƴan Najeriya ba za su iya mantawa da lokacin da hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS), ta yi yunƙurin ɗaukar ma'aikata a faɗin ƙasar nan a ranar 15 ga watan Maris, 2014.
Miliyoyin masu neman aiki sun garzaya cibiyoyin zana jarabawa a faɗin ƙasar nan, ciki har da birnin tarayya Abuja.
Aƙalla mutane 16 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan da dama sun jikkata sakamakon cunkoson jama’a da turmutsutsi.
Yawancin waɗanda suka mutu sun rasu ne a Abuja, Port Harcourt, Minna da Benin.
4. Turereniya a cocin Port Harcourt
A ranar 28 ga watan Mayu, 2022, sama da mutane 31 ne aka tabbatar da mutuwarsu a birnin Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, sakamakon turmutsutsi a wurin wani taron coci.
Cocin Kings Assembly ta shirya shirin ‘Shop for Free’, inda ake sa ran mahalarta taron za su samu kayan abinci kyauta.
Abubuwan da za a raba na kyauta sun sanya mutane suka yi tururuwa zuwa wajen.
5. Turmutsutsi a cocin Legas
A ranar 18 ga watan Agusta, 2022, mutane biyu sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata sakamakon turmutsutsi a Cocin Comfort Life Mission International Church da ke unguwar Ikotun a jihar Legas.
An ce lamarin ya auku ne bayan da masu ibada kashi na biyu suka yi ƙoƙarin shiga cikin cocin.
6. Rabon shinkafar Kwastam
A ranar 23 ga watan Fabrairu, 2024, aƙalla mutane bakwai ne suka mutu a lokacin rabon buhunan shinkafar da hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta ƙwace a Legas.
Ƴan Najeriya da dama ne suka garzaya ofishin hukumar NCS da ke unguwar Yaba a Legas domin sayen shinkafar, lamarin da ya yi sanadiyyar aukuwar turmutsutsi.
7. Rabon tallafi a jami'ar Nasarawa
A ranar 22 ga watan Maris, ɗalibai uku na jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) suka mutu a wani turmutsitsin da ya faru a lokacin rabon shinkafa da gwamnatin jihar ta bayar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗalibai da dama sun samu raunuka a yayin da lamarin ya auku.
8. Rabon zakka a Bauchi
A ranar 23 ga watan Maris, 2024, an tattake mutane bakwai har lahira yayin wani rabon zakka a kamfanin Shafa Holdings Plc da ke hanyar Jos a Bauchi.
An kuma jikkata mutane da dama yayin rabon sadakan da kamfanin ya shirya.
Mutum 22 sun rasu a turmutsutsin Anambra
A wani labarin kuma, kun ji cewa adadin mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon turmutsutsin da ya auku a jihar Anambra ya ƙaru.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya bayyana cewa adadin mutanen da suka rasu ya kai mutum 22, inda ya ƙara da cewa sun fara gudanar da bincike kan lamarin.
Asali: Legit.ng