An Caccaki Tinubu kan Warewa Buhari da Tsofaffin Shugabanni N27bn a 2025
- Jam'iyyun adawa sun yi Allah wadai da makudan kudin da aka ware a kasafin shekarar 2025 ga tsofaffin shugabanni
- Daga cikin wadanda za su amfani akwai tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da mataimakansu
- Jam'iyyun PDP da NNPP na ganin duk cikin shugabannin, babu wanda ba shi da biliyoyin Naira mallakin kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki da manyan jam’iyyun adawa a kasar sun samu sabani kan ware makudan kudade har N27bn da gwamnatin tarayya ta ware domin tsofaffin shugabanni.
Sauran wadanda za su amfana da kudin sun hada da mataimakan shugabanni, shugabannin gwamnati, shugabannin ma’aikata na baya da farfesoshi a kasafin 2025.
Jaridar Punch ta ce za a ba tsofaffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari wani kaso na N27bn da aka ware masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma tsofaffin mataimakan shugabanni da su ka hada da Atiku Abubakar, Namadi Sambo, da Farfesa Yemi Osinbajo da tsofaffin shugabannin mulkin soja.
Jam'iyyar PDP ta soki Bola Tinubu
Mataimakin Shugaban Matasa na Kasa na jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor, ya bayyana cewa miliyoyin ’yan Najeriya ne suke bukatar kudaden, ba tsofaffin shugabanni ba.
Ya ce;
“A tarihin kasar nan, ban ga wanda ba ya da biliyoyin kudi daga cikin Jonathan, Obasanjo, Atiku ko IBB ba.”
NNPP ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu
Sakataren yada Labarai na jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya ce babu dalilin ware makudan biliyoyin Naira domin tsofaffin shugabann yayin da jama’a ke fama da wahala.
Johnson ya koka cewa kasafin ya nuna kara cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba shi da masaniyar halin da ’yan kasa ke ciki na kunci da tsadar rayuwa
“Abin da zan iya cewa shi ne, gaba daya, kasafin ya ba mu damar fahimtar yadda wannan gwamnati ke rashin damuwa da halin da jama’a ke ciki.”
An ware biliyoyi domin tafiye-tafiyen Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 9.36 a kasafin shekarar 2025 domin tafiye-tafiye, ciye-ciyen shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa.
A cikin kudin, an ware wa shugaba Tinubu Naira biliyan 6.14 na tafiye-tafiye, N431.6m na girke-girke, yayin da aka ware wa Kashim Shettima Naira 1.31 domin tafiye-tafiye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng