Yunwa ba Kyau: Yan Bindiga Sun Tare Hanya, Sun Kwace Kayan Abincin Kirismeti a Kaduna

Yunwa ba Kyau: Yan Bindiga Sun Tare Hanya, Sun Kwace Kayan Abincin Kirismeti a Kaduna

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kwace kayan abinci da abin sha daga hannun wani mutum a kan babur
  • Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024 a Kaduna yayin da mutumin ya dawo daga siyan kayan abinci
  • Ba a ji wa mutumin rauni ba, amma yan bindigar sun tsere da kayan a kan babur ba tare da an kama su ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Yan bindiga sun kwace kayan abinci da abin sha daga hannun wani mutum a kan babur a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a kauyen Gidan Abe da ke Kachia a jihar Kaduna a ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024.

Yan bindiga sun tare hanya inda suka kwace kayan abincin Kirsimeti
Yan bindiga sun kwacewa wani mutum kayan abincin Kirsimeti a jihar Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun kwace kayan abincin Kirsimeti

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbe jariri dan shekara 1 da mutane da dama

Wani jagoran al’umma daga yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Daily Trust a jiya Litinin 23 ga watan Disambar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:23 na yamma, lokacin da mai babur din ya siyo buhun shinkafa, abin sha da kayan miya.

An ce mutumin ya fito daga Katari yana kan hanyarsa ta zuwa kauyen Gidan Abe don Kirsimeti, sai yan bindiga a kan babur suka tare shi.

Wani jagoran al'umma ya tabbatar da lamarin

Yan bindigar sun kwace kayan abincin daga hannunsa ba tare da sun ji mashi ciwo ko sun yi yunkurin sace shi ba.

“Da safiyar yau na samu labarin cewa yan bindiga a Katari sun kwace kayan abinci daga hannun wani mutum da ke kan babur."

- Cewar majiyar

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu karin bayani daga jami’an tsaro musamman yan sanda kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da wata tankar mai ta tarwatse ana cikin jimamin rasa rayuka a Abuja

Yan sanda sun dakile harin yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Kaduna, sun samu nasarori kan masu tayar da ƙayar baya.

Ƴan sandan sun daƙile yunƙurin kai wani hari na ƴan bindiga tare da cafke wasu da ake zargi da yin fashi da makami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.