Hauhawar Farashi: Tinubu Ya Fadi Shirin Gwamnatinsa a kan Rage Tsadar Kayayyaki

Hauhawar Farashi: Tinubu Ya Fadi Shirin Gwamnatinsa a kan Rage Tsadar Kayayyaki

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nesanta gwamnatinsa da kokarin kayyade farashin kaya a kasuwanni
  • Ya ce gwamnatinsa ba za ta kayyade farashi ba, amma za ta dauki matakin da zai tabbatar da farashin kaya ya sauka da kansa
  • Bola Tinubu ya bayyana matsayarsa a lokacin da ake ci gaba da samun hauhawar farashin kayayyaki har sama da 200%

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matakin da gwamnatinsa ta ke shirin dauka a kan batun hauhawar farashi daya jefa rayuwar ‘yan Najeriya a cikin wahala.

Shugaban, a tattaunawarsa ta farko da ‘yan jarida tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023 ya tabbatar da masaniya a kan yadda ake samun tsadar kayan amfanin yau da kullum.

Kara karanta wannan

Radadin cire tallafi: Tinubu ya fadi yadda abokinsa ya gagara rike manyan motoci 5

Tinubu
Tinubu ya yi watsi da kayyade farashi Hoto; Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa farashin kayan abinci ya ci gaba da karuwa da 200% tun bayan da Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban Najeriya a watan 29 Mayu, 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi watsi da daidaita farashi

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba ya goyon bayan daidaita farashin kayan masarufi domin sa wa hauhawar farashi linzami.

Ya bayyana haka ne a yammacin ranar Litinin ga manema labarai, inda ya kara da cewa gwammnatinsa za ta bar ‘yan kasuwa da farashinsu da su ka kayyade.

Matakin gwamnatin Tinubu a kan hauhawar farashi

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida matakin da gwamnatinsa ta ke ganin shi ne zai magane matsalar hauhawar farashi a cikin kasuwannin kasar.

Ya ce abin da gwamnatinsa za ta yi shi ne ta cigaba tabbatar da wadata kasuwanni da kayayyakin da ake bukata, wanda za isa farashin ya sauko da kansa.

Kara karanta wannan

'Ku koyi rayuwa a haka': Tinubu ya ba yan Najeriya satar amsa kan tsadar wutar lantarki

Tinubu ya kara da cewa;

“Ba na goyon bayan daidaita farashi. Ina ba da hakuri. Abin da ya kamata mu yi shi ne mu ci gaba da samar da kayayyaki a kasuwa.”

Tinubu ya magantu a kan cire tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a kan bakarsa na cire tallafin man fetur, wanda shi ne abu na farko da ya ayyana bayan karbar rantsuwar aiki.

Shugaban kasar wanda ya fadi haka a Legas ya jaddada cewa matakin cire tallafin mai ya zama dole, ganin yadda kudin tallafin da biya ya yi wa tattalin arzikin Najeriya nauyi matuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.