Yadda Hukumar EFCC Ta Yi Farautar Manyan 'Yan Siyasar Najeriya a Shekarar 2024
Hukuma mai yaki da yi wa tallafin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar wasu manyan 'yan siyasar Arewa a shekarar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Hukuma mai yaki da yi wa tallafin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta yi fadi tashi wajen kamawa da gurfanar 'yan siyasa a 2024.
Daga cikin wadanda ta gurfanar kan zargin karkatar da kudi sun hada da tsofaffin gwamnoni, ministoci da sauransu.
A wannan rahoton, mun tattaro muku rahoto a kan jerin manyan 'yan siyasa 5 da EFCC ta gurfanar a shekarar 2024 daga Arewacin Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan siyasar da EFCC ta gurfanar a 2024
1. Saleh Mamman
An gurfanar da tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, a ranar 11 ga watan Yuli kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi hada baki wajen karkatar da Naira biliyan 33.8.
Ana zarginsa da karkatar da kudin da aka ware domin ayyukan wutar lantarki na Zungeru da Mambilla, wanda hakan ya sa ayyukan suka tsaya cik.
2. Hadi Sirika
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika yana fuskantar tuhume-tuhume akalla biyu da suka hada da bayar da kwangilolin bogi da karkatar da kudi.
An gurfanar da shi tare da 'yarsa da surukinsa a ranar 9 ga watan Mayu bisa zargin bayar da kwangila ta Naira biliyan N1.5 don aikin fadada filin jirgin saman Katsina.
The Cable ta rahoto cewa a wata tuhuma daban, an gurfanar da Sirika tare da dan uwansa kan bayar da kwangila ta Naira biliyan 19.4 ga wani kamfani mallakar dan uwansa.
3. Abdulfatah Ahmed
Tsohon Gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya fuskanci tuhume-tuhume guda 14 da suka hada da almundahana da karkatar da kudaden jama’a.
Ana zarginsa da sace kudaden albashin malamai da kuma kudaden tsaro a lokacin da yake gwamna.
EFCC ta ce Ahmed ya karkatar da kudade har Naira biliyan 5.78 tare da hadin gwiwar tsohon kwamishinan kudin jihar, Demola Banu.
4. Darius Ishaku
An gurfanar da tsohon Gwamnan Taraba, Darius Ishaku, a ranar 30 ga watan Satumba bisa tuhume-tuhume 15 da suka hada da cin amanar jama’a da karkatar da kudaden gwamnati.
Ana zargin Ishaku da karkatar da makudan kudi tare da hadin gwiwar tsohon sakataren na ma’aikatar kananan hukumomin jihar, Bello Yero.
A lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023, an zarge shi da almundahana kan wasu ayyuka da aka ce ba su cika ka’ida ba.
5. Yahaya Bello
An gurfanar da tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, a ranar 13 ga watan Disamba bisa tuhume-tuhume 19 da suka hada da almundahana da karkatar da sama da Naira biliyan 80.
Yahaya Bello da ya shahara wajen kauce wa gurfanarwa, ya samu beli na Naira miliyan 500 kuma an kafa masa sharudan beli.
Hukumar EFCC ta gayyaci ciyamomi a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gayyaci dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar Edo bayan dakatar da su da aka yi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan jihar Edo ne ya jagoranci dakatar da su a kan zargin rashin aiki da kudin gwamnati yadda ya kamata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng