Likitoci Sun Sanya Ranar Tsunduma Yajin Aiki, Sun Yi wa Ministan Tinubu Barazana
- Likitoci sun yi wa Nyesom Wike barazanar tsunduma yajin aiki mafi muni a Abuja idan ba a biya bukatunsu ba cikin mako biyu
- Bukatu likitocin sun hada da biyan albashin watanni shida, biyan kudin kayan aiki da kuma gyaran dokar 'bonding'
- Likitocin sun ce rashin adalcin da ake yi masu zai iya rusa tsarin kiwon lafiya, sun nemi Wike ya gaggauta warware matsalar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar Likitoci ta ARD-FCTA ta gargadi ministan Abuja, Nyesom Wike, kan cewa za ta fara yajin aiki mafi muni cikin kwanaki 14 idan ba a biya bukatunsu ba.
Shugaban kungiyar, Dakta George Ebong, yayin jawabi ga manema labarai a Abuja, ya yaba wa Wike kan ayyukan ci gaban gine-gine, amma ya nemi ya kula da walwalar likitoci.
Likitoci na barazanar shiga yajin aiki
Dakta Ebong ya ce akwai bukatar Wike ya mayar da hankali kan ci gaban likitoci kamar yadda yake yi a bangaren gine-gine, a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ARD-FCTA ta ce Wike na da kwanaki 14 kacal don daukar mataki kan bukatunta, ko kuma ta shiga yajin aiki mafi muni a asibitocin Abuja.
Dakta Ebong ya shaida cewa:
“Likitoci sun koma saniyar ware. Yayin da yake gyara gine-gine, ya kamata ya gyara halin da muke ciki a bangaren walwala.”
Likitoci sun mika bukatu ga Wike
Kungiyar ta nemi ministan ya gaggauta biyan albashin watanni shida da aka rikewa 'ya'yanta da aka dauka aiki a shekarar 2023.
Ta kuma bukaci a biya kudin horarwar likitoci na 2024 tare da sake duba dokar 'bonding policy' daga shekara shida zuwa biyu.
Haka kuma, kungiyar na son a tabbatar da doka kan biyan kudin tsallake ma'aunin albashi, tare da baiwa mambobinta na 2023 takardar tsallake ma'aunin.
Abin da zai faru nan da mako 2
Bukatun likitocin sun hada da biyan kudin kayan aiki na 2024, kudin hadari na wata 13 na shekarar 2023 da kuma kara daukar ma’aikatan lafiya a Abuja.
Dakta Ebong ya ce idan aka cigaba da wannan rashin adalcin, tsarin kiwon lafiya na kasa zai rushe, kuma bukatar da suka gabatar ce za ta warware matsalar.
Ya yi kira ga ministan Abuja da ya dauki mataki cikin kwanaki 14, domin kaucewa yajin aiki mafi muni wanda ka iya haifar da asarar rayuka a asibitocin Abuja.
Likitoci sun tafi yaji aiki kan sace likita
A wani labarin, mun ruwaito cewa likitoci karkashin kungiyar NARD sun tsunduma yajin aikin gargadi kan sace wata likita da aka yi a jihar Kaduna.
Kungiyar NARD ta bukaci gwamnati da ta gaggauta sa baki don ganin an sako Dakta Ganiyat Papoola da aka yi garkuwa da ita tun a shekarar da ta gabata.
Asali: Legit.ng