Gwamna Ya Bukaci Shugabannin Kananan Hukumomi Su Yi Murabus, Ya Fadi Laifinsu
- Ma'aikatan ƙananan hukumomi a jihar Ebonyi sun shiga wani hali bayan an kwashe watanni ba a ba su albashinsu ba
- Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya nuna damuwarsa kan jinkirin da aka samu wajen biyan ma'aikatan kuɗadensu
- Francis Nwifuru ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin da su yi murabus idan ba za su iya biyan ma'aikatan haƙƙoƙinsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana damuwarsa kan jinkirin biyan albashi da fansho ga ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar.
Gwamna Nwifuru ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin da su yi murabus idan ba za su iya biyan kuɗaɗen ba.
Gwamnan Ebonyi ya damu kan rashin biyan albashi
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Monday Uzor, cewar rahoton jaridar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nwifuru ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, sannan ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi 13 na jihar, da su tabbatar da cewa an biya kuɗaɗen kafin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Litinin 23 ga watan Disamba, 2024.
Gwamna Nwifuru ya jaddada ƙudirinsa na ganin an samar da shugabanci nagari, inda ya bayyana cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen kyautatawa jama'a.
Gwamna Nwifuru ya ba ciyamomi wa'adi
"Ya kamata dukkanin ma'aikatan ƙananan hukumomi su samu albashinsu da fansho ya zuwa ƙarfe 2:00 na ranar Litinin."
"Mun ƙudiri aniyar gudanar da kyakkyawan shugabanci ga jama’ar mu. Idan kuna tare da mu, ku zo a haɗa kai cikin abin da muke yi, idan ba ku tare da mu, ku san inda dare ya yi muku."
"Idan har zuwa ƙarfe 2:00 na rana ba a biya ma’aikatan albashin Oktoba da Nuwamba ba, shugabannin ƙananan hukumomin su yi murabus."
- Gwamna Francis Nwifuru
Ma’aikatan kananan hukumomin jihar Ebonyi dai na bin bashin albashin watan Oktoba da Nuwamba, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Majalisa ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Edo ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin jihar tare da mataimakansu.
Majalisar dokokin ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin ne na tsawon wata uku bayan sun gaza kawo rahoton yadda suka kashe kuɗaɗensu.
Asali: Legit.ng