Wike Ya Shirya Tatsar N30bn daga Masu Filaye a Abuja, An Sanya Wa'adin Biyan Kudin

Wike Ya Shirya Tatsar N30bn daga Masu Filaye a Abuja, An Sanya Wa'adin Biyan Kudin

  • Hukumar gudanarwar Abuja ta fara harin tara Naira biliyan 30 daga manyan kasar nan da kamfanoni da suka mallaki filaye
  • A baya dai, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da wa'adin mako biyu ga masu filayen da su biya kudaden da ake biyansu
  • Ya bayyana hukuncin da aka shirya dauka matukar masu filaye da kamfanonin su ka yi biris da umarnin da hukuma ta ba su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya fara shirin tattaro akalla N30bn daga mutane 1,376 da kuma kamfanoni.

Wadanda ake sa ran za su biya wannan makudan kudi su ne su ka da gaza biyan kudin takardun mallakar kadarori a unguwannin Maitama, Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda aka shigowa 'yan ta'adda tankar yaki daga Libya zuwa Arewacin Najeriya

Nyesom
Wike na shirin samun N30bn daga masu filaye a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Wani labari da ya kebanta da Premium Times ya nuna cewa hukumar gudanarwar FCTA ta fitar jerin mutane 762 da ba su biya komai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin da Abuja ke bin masu kadarori

Ana sa ran mutane za su biya N22.8b, yayin da ake sa ran N11.6b daga mutane 614 da ba su kammala biyan kudin takardun filayensu ba.

Mutane 614 sun riga sun biya N3.1b daga cikin N11b da hukumar gudanarwar Abuja ta bukata su biya na daga cikin abin da hukumomin ke binsu.

Jerin masu biyan Abuja kudin filaye

A sahun gaba na wadanda ba su biya ko sisi ba sun haɗa da kamfanin Quality Real Estate Investment Limited (N5.9bn).

Akwai gidauniyar Muhammadu Buhari Trust Foundation (N1.2bn);.kamfanin M .O Real Estate & Construction Company (N709m).

Sai kamfanin Bil & Labily Limited (N634m); Jordan Farms & Estate Limited (N298m); Hyperstation Limited (N281m); da Emirate Luxury Suite Limited (N139m) da wasu jerin kamfanoni 16.

Kara karanta wannan

"Mun samu nasara:" Sanata Ndume ya fadi amfanin watsi da kudirin harajin Tinubu

An karyata karbe filin Buhari a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa Garba Shehu, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi karin haske kan rahoton kwace filinsa Abuja.

Garba Shehu ya ce filin da aka kwace ba na tsohon shugaban ba ce, amma na wata Gidauniya ce ta magoya bayansa suka siya masa, ya fadi abin da ya ke tunanin ya haddasa kwace filin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.