Zaratan 'Yan Najeriya 50 za Su je Fatakwal domin Gano Gaskiya a Matatar NNPCL

Zaratan 'Yan Najeriya 50 za Su je Fatakwal domin Gano Gaskiya a Matatar NNPCL

  • Kungiyoyin fararen hula za su kai ziyara ta musamman domin tantance gaskiyar cewa matatar man Najeriya ta Fatakwal ta fara aiki
  • Rahotanni sun nuna an kafa kwamiti mai mutum 50 domin zuwa matatar da kuma bincike kan hakinanin yadda aikin tace mai ke gudana
  • An ruwaito cewa kungiyar da ta fitar da sanarwar ta ce za a fitar da rahoton bincike ga al'umma bayan kammala aikin tantancewar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar National Civil Society Coalition (NCSCN) ta sanar da shirinta na kai ziyara ta musamman matatar Fatakwal a watan Janairun 2025.

Kungiyar ta kafa kwamiti na mutum 50 domin gudanar da aikin tare da tantance sahihancin rahotannin aikin matatar.

Matatar fatakwal
Tawaga za ta ziyarci matatar Fatakwal domin gano gaskiya. Hoto: NNPC Limited
Asali: Twitter

Punch ta ruwaito cewa shugabar NCSCN, Blessing Akinsolotu, ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole saboda wasu rahotanni da ke kawo shakka kan aiki da nagartar matatar.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rasa rayuwa a turereniyar karbar kayan tallafi a Abuja, wasu suna asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rudani kan fara aikin matatar Fatakwal

A watan Maris na 2021 aka amince da kashe Dala biliyan 1.5 domin gyara matatar mai ta Fatakwal, wacce aka sake kaddamarwa a ranar 26 ga Nuwamba, 2024.

Shugaban NNPC, Mele Kyari ne ya jagoranci kaddamarwar kuma kamfanin ya samu yabo daga 'yan Najeriya.

Sai dai an cigaba da samun rudani kan aikin matatar inda wasu rahotanni ke cewa ba a fara tace mai ba wasu kuma suka ce an tsayar da aiki a matatar.

Tawagar mutum 50 za ta je matatar Fatakwal

Kungiyar NCSCN ta ce ziyarar tantancewar za ta samar da kwakkwaran bayani kan adadin man da ake sarrafa wa da kuma yadda ake gudanar da aiki a matatar.

Tribune ta wallafa cewa NCSCN ta yi alkawarin wallafa duk wani rahoto da aka gano bayan ziyarar tantancewar ga jama’a da duniya baki daya.

Kara karanta wannan

NNPCL ya rufe matatar Fatakawal da gwamnati ta gyara kwanan nan? Gaskiya ta fito

Ta kara da cewa yunkurin zai kara tabbatar da gaskiya da kuma kawar da shakku game da aiki da ingancin matatar mai ta Fatakwal.

An rage farashin man fetur a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta bayyana cewa za ta fara sayar da mai a farashi mai rahusa a yau.

Kungiyar IPMAN ta ce hakan na zuwa ne bayan yarjejeniya da suka yi da matatar Dangote a kan samun saukin farashin man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng