Limami: "Dalilin da Ya Sa Aka Liƙa Banar Yesu ba Allah ba ne a Masallacin Legas"

Limami: "Dalilin da Ya Sa Aka Liƙa Banar Yesu ba Allah ba ne a Masallacin Legas"

  • Limamin Masallacin Lekki ya ce ba a lika banar 'Yesu ba Allah ba ne' a jikin bangon masallacin don tada zaune tsaye ba
  • Bayan banar ta jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, gwamnati ta roki a cire ta don zaman lafiya, musamman a lokacin Kirsimeti
  • Ridwanullah Jamiu ya ce sun cire banar a yanzu amma za su gyara su saje mayar da ita, yana mai fadin dalilin likta tun farko

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Babban limamin Masallacin Lekki, Ridwanullah Jamiu, ya ce ba a lika banar "Yesu Almasihu ba Allah ba ne" a masallacin don tunzura mutane ba.

Legit Hausa ta rahoto cewa banar da aka lika a jikin katangar masallacin ta jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, inda wasu ke ikirarin cewa an ci zarafin addinin Kirista.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da manyan Najeriya sun hallara Jigawa auren 'yar gwamna Umar Namadi

Limamin masallacin Lekki ya fadi dalilin lika banar Yesu ba Allah ba ne
Limamin masallacin Lekki ya yi magana kan banar Yesu ba Allah ba ne da suka lika. Hoto: @tosinraj
Asali: Twitter

Dalilin lika banar Yesu a jikin masallaci

A wani bidiyo da MS Ingawa ya wallafa a shafinsa na X, an ji limamin masallacin yana cewa, an lika banar ne domin ilimantar da Musulmi kan akidar addininsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Liman Ridwanullah Jamiu ya ce:

“Idan ka zo masallacin Lekki, za ka koyi wani abu. Akwai allunan sako na ilimi a waje da suke ilimantar da mutane.”

Jamiu ya ce duk banar da aka sanya a wajen masallacin suna dauke ne da ayoyin Al-Qur’ani da Hadisai domin fadakar da Musulmi.

"Gwamnati ta roki a cire banar" - Jamiu

Limamin ce bayan hoton daya daga cikin banonin ya bazu, ya samu kiran gwamnati da hukumomi suna rokon a cire banar saboda bukukuwan Kirsimeti.

Ya kara da cewa ba a lika banar don tada zaune tsaye ba, yana mai cewa akwai bambanci tsakanin wa'azi da tayar da hankali.

“Wannan banar ta dauki fiye da wata biyu a wurin, ba mu yi nufin mu jawo wata fitina ba, mu mutane masu son zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

'Abu ya zo da ƙarar kwana': Wani jami'an tsaro ya riga mu gidan gaskiya a bakin aiki

- A cewar limamin.

Za a sake lika banar Yesu a masallacin

Jamiu ya jaddada cewa babu wanda ba zai yi tutiya da Yesu ba, domin Musulmi ma suna da akidar su game da shi bisa Qur’ani wanda ya kira shi Isah.

Limamin ya ce:

“Dukkan abin da Musulmi suka yarda da shi dole ya dace da Al-Qur’ani, wanda ya ce Yesu ba Allah ba ne, manzon Allah ne.”

Game da cire banar, Jamiu ya ce sun yi hakan don zaman lafiya, don su mutunta gwamnati, tare da jaddada cewa za su gyara sakon sannan su sake likawa.

Kalli bidiyon a kasa:

An cire banar Yesu ba Allah ba ne

Tun da fari, mun ruwaito cewa mahukuntan babban masallacin Juma'a na Lekki da ke jihar Legas sun cire banar 'Yesu ba Allah ba ne' da ta jawo ce-ce-ku-ce.

Shafukan sada zumunta sun cika da surutu kan wannan bana da aka gani a jikin masallacin, inda aka cire ta bayan korafi ya yi yawa da kuma rokon gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.