An Shiga Tashin Hankali: Bello Turji Ya Kafa Sabon Sansanin Ta'addanci a Jihar Sokoto

An Shiga Tashin Hankali: Bello Turji Ya Kafa Sabon Sansanin Ta'addanci a Jihar Sokoto

  • Bello Turji ya kafa sabon sansani a dajin Indaduwa kusa da Gundumi, wanda ya zama cibiyar hare-haren 'yan bindiga a yankin
  • Rikici da kungiyar Maniya ya sa Turji kafa sansanin, inda ya ke neman karya karfinsu a da kuma yaki da sauran jami'an tsaro
  • Ana zargin Turji da yin garkuwa da mutane sama da 40, tare da tsare su a Indaduwa, yayin da ake karbar kudin fansa a sabon salo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Rahotanni sun nuna cewa shugaban 'yan bindiga Bello Turji ya kafa sabon sansani a dajin Indaduwa, kusa da kauyen Bula, cikin Gundumi.

Wannan sabon sansanin, wanda aka kafa makonni uku da suka wuce, ya shahara wajen hare-haren 'yan bindiga, ciki har da toshe hanyar Isa-Marnona.

Majiyoyi da dama sun yi magana kan sabon sansanin da Bello Turji ya kafa a Sokoto.
Bello Turji ya kafa sabon sansani a Sokoto, ya zafafa kai hare hare. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, musamman Arewacin kasar ya fitar da rahoton a shafinsa na X a ranar 22 ga Disambar 2024.

Kara karanta wannan

An kona makarantar Kandahar a Bauchi: Rigima ta kaure tsakanin matasa da ƴan CJTF

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Turji ya kafa sabon sansani a Sokoto

Majiyoyi sun tabbatar da cewa sansanin Indaduwa na da alaka da kai farmaki, yin garkuwa, da aikata miyagun laifuka a kan matafiya da mazauna yankin.

Ana zargin cewa wasu mutanen Illela da Marnona suna taimaka wa kungiyar Turji ta hanyar saukaka karbar kudin fansa da bayar da bayanai.

A daren 21 ga Disamba ne aka rahoto cewa 'yan kungiyar Turji sun kai hari ga jami'an tsaro a hanyar Gundumi-Isa.

Ana fada tsakanin Turji da kungiyar Maniya

Shaidu sun ce kungiyar ta yi amfani da amfani da shirin kwanton bauna wajen kai hari mai muni sannan suka tsere zuwa cikin dajin.

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa akwai manyan dalilai guda biyu na kafa wannan sansanin.

Rikici da wata kungiyar Maniya ya haifar da sansanin, wanda ya samo asali daga rikicin da Turji ya gada daga mahaifinsa, Rugga Chida.

Amfanin sabon sansanin ga Bello Turji

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Wannan rikicin ya haifar da rikici mai muni da ya kashe Kachalla Dullun, wanda ke da tasiri a cikin kungiyar Maniya.

Turji na kallon sabon sansanin a matsayin hanya ta karya karfin kungiyar Maniya a yankin Dutsin Gwauro.

Ana ganin hare-haren baya-bayan nan a matsayin kokarinsa na hana gwamnati kafa sansanin tsaro a Gundumi.

Yaran Bello Turji sun koma sabon sansanin

Manyan 'yan kungiyar Turji, irin su Dan Kwaro, Ila Manawa, Duna da Sani Black, sun mayar da hankulansu zuwa wannan sabon sansanin.

Kungiyar tana da ikon kai hare-hare zuwa yankunan da ke kusa da Galadi, Maradun, Gundumi da Raba, inda ake tsare mutane sama da 40.

An ce kudin fansa suna zuwa ta hannun masu bayar da rahoto a Marnona da Gidan Rana, yayin da wadanda aka sako suka tabbatar da ayyukan kungiyar a yankin.

Zamfara: An kama malamin 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa malamin addini da ke yi wa 'yan bindiga shiri da ba su sa'a idan za su fita ta'addanci a Zamfara da Katsina ya shiga hannu.

Kara karanta wannan

An cafke fitaccen mawakin siyasa a Kano, an zargi yan Kwankwasiyya da hannu

Kungiyar 'yan bangar Zamfara sun cafke malamin mai shekaru 72 bayan samun sahihan bayanai, inda kuma malamin ya amsa laifinsa a cikin wani bidiyo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.