Yadda Aka Shigowa 'Yan Ta'adda Tankar Yaki daga Libya zuwa Arewacin Najeriya
- Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da wasu mutane da ake tuhuma da safarar makamai ga 'yan ta'adda a kotun tarayya a Abuja
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ana zargin mutanen da shigo da motar yaki daga Libya a kan kudi Naira miliyan 28.5
- Haka zalika ana zarginsu da laifin bayar da kayan gina gida da kayan aiki ga sansanonin 'yan ta’adda a jihohi daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - A yau Litinin za a gurfanar da wasu mutane da ake zargi da laifin ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ana tuhumar mutanen ne da laifuffukan da suka hada da shigo da motar yaki daga kasar Libya, da kuma bayar da tallafi ga sansanonin ta’adda.
Rahoton Punch ya tabbatar da cewa gwamnati ta shigar da tuhume-tuhume 11 a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a kan wadanda ake zargin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka shigo da motar yaki daga Libya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wadanda ake tuhuma sun shigo da motar yaki ta sojoji daga Libya zuwa jihar Zamfara a shekarar 2021.
Vanguard ta wallafa cewa sun biya Naira miliyan 28.5 kudi a hannu da kuma amfani da banki domin mallakar motar.
Rahoton ya kara da cewa an mallakar da motar a hannun wani shugaban 'yan ta’adda, Kachalla Halilu, domin gudanar da hare-haren ta’addanci.
Yadda aka taimaki 'yan ta'adda a jihohi
Ana zargin wadanda ake tuhuma da samar da kayayyaki, ciki har da buhunan siminti, kwanon rufin gida da rodi ga sansanonin 'yan ta’adda a jihohin Zamfara, Sokoto da Kaduna.
Har ila yau, an gano cewa sun samar da wasu kayayyaki masu muhimmanci ga 'yan ta'adda domin saukaka musu kai hare-hare.
'Yan ta'adda sun fafata a tsakaninsu
A wani rahoton, kun ji cewa kazamin fada ya kaure tsakanin 'yan ta'adda wanda ya jawo asarar rayuka da raunata wasu a cikinsu.
Fadan ya jawo mutuwar manyan shugabannin 'yan ta'adda uku yayin da miyagun suka gwabza da juna a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng