"Mun Samu Nasara:" Sanata Ndume Ya Fadi Amfanin Watsi da Kudirin Harajin Tinubu
- Sanata Ali Ndume ya kafe a kan bakarsa na neman gwamnati ta janye kudirin harajin da ta aika don samun amincewarsu
- Wannan na zuwa bayan kudirin ya samu tsaiko saboda kakkausan suka ga kudirin da aka samu daga wasu 'yan majalisa
- A karin bayaninsa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa jayayya da kudirin ya fara ba da sakamakon da ake bukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa fafutuka da ya rika yi ta nusar da jama'a illar kudirin harajin Tinubu ya fara haifar da da mai ido.
'Dan majalisar ya ce dagewarsa kan janye kudirin gyaran haraji da aka tura Majalisar dattawa shi ne ya bude kofar gyare-gyare a kudirin.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tsohon bulaliyar majalisa ya fadi haka ne a babban birnin tarayya Abuja inda ya ce dole a ci gaba da duba kudirorin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kudirin harajin Tinubu zai shafi kowa," Ndume
Jaridar Thisday ta ruwaito cewa Sanata Ali Ndume ya ce har yanzu ya na kan bakarsa na cewa a janye kudirin haraji har sai an kammala tattaunawa a kanta.
Ali Ndume ya ce;
“Wadanda ke ganin cewa gyaran haraji na yanzu yana cutar da Arewacin Najeriya kawai ba su da masaniya. Wannan dokar tana cutar da duk ‘yan Najeriya masu karamin albashi da matsakaici.”
"Arewa ba ci ma zaune ba ce," Sanata Ndume
Sanata Ali Ndume da ke wakilta Borno ta Kudu a Majalisar dsttawa ya karyata zargin cewa Arewacin Najeriya ci ma zaune ce kawai.
Ya ce yadda lamarin ya ke shi ne, dukkan sassan Najeriya suna bukatar juna don samun ci gaba da dorewa, kuma Arewa na da rawar takawa.
Ndume ya fara adawa da kudirin harajin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa yadda Sanata daga Borno, Ali Ndume ya ce ba zai amince da kudirin shugaban kasa, Bola Tinubu ya bijiro da shi na gyare-gyaren haraji ba.
Ya bayyana dalilinsa da cewa lokacin ya yi tsauri, ganin yadda 'yan Najeriya su ke fama da tsananin rashin, inda ya nemi goyon bayan wasu daga cikin 'yan majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng