Gwamnatin Tarayya Ta Dage Haramcin Hakar Ma'adanai a Zamfara, Ta Fadi Dalili
- Ɓangaren haƙar ma'adanai a Zamfara zai farfaɗo yayin da gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumin da aka sanya masa a 2019
- Ministan ma'adanai, Dele Alake, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ɗage haramcin haƙar ma'adanai a jihar Zamfara
- Dele Alake ya yi nuni da cewa an yi hakan ne bayan samun ƙaruwar yanayin tsaro mai kyau a jihar da ake fama d a'yan bindiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ɗage haramcin haƙar ma’adanai a jihar Zamfara.
A shekarar 2019, gwamnatin tarayya ta hana ayyukan haƙar ma'adanai a Zamfara, sannan ta umarci ƴan ƙasashen da ke cikin wuraren haƙar ma'adanai a jihar da su fice daga yankin nan take.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa ministan ma'adanai, Dele Alake, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka ɗage haramcin hako ma'adanai?
Ministan ya bayyana cewa gaggarumin ci gaban da aka samu a harkokin tsaro a faɗin jihar Zamfara ne dalilin ɗage dokar, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Dele Alake, ya ce Najeriya na da tarin ribar da za ta samu daga farfaɗo da ayyukan haƙar ma'adanai a Zamfara wacce ke cike da ɗimbin zinare, lithium da tagulla.
Alake ya yi nuni da cewa, haramcin da aka yi a baya, wanda ke da kyakkyawar niyya, ya haifar da giɓin da masu haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, suka yi amfani da shi wajen kwashe albarkatun ƙasar nan.
"An kawar da barazanar da ke akwai ta rayuka da dukiyoyi wacce ta sanya aka sanya haramcin a 2019. Ƙoƙarin jami'an tsaro ya sanya an samu raguwar matsalar rashin tsaro."
"Yanzu da aka ɗage haramcin haƙo albarkatun ƙasar, ɓangaren haƙar ma'adanai na Zamfara zai fara samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar nan."
- Dele Alake
Ministan ya ƙara da cewa dage haramcin zai kuma taimaka wajen daidaita ayyukan hakar ma'adinai a jihar.
Rami ya rufta da masu hakar ma'adanai
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan bayan wani ramin da ake haƙar ma'adanai ya rufta da mutane a jihar Zamfara.
Mutane akalla uku ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon aukuwar lamarin a wani ƙauye na ƙaramar hukumar Anka da ke Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng