IPMAN da Matatar Dangote Sun Shiga Yarjejeniyar Rage Farashin Fetur zuwa N935
- Kungiyar dlillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta tabbatar da cewa 'ya'yanta za su fara sayar da litar fetur a kan sabon farashi
- IPMAN ta sanar da cewa wannan ya biyo bayan yarjejeniya da su ka yi da matatar Dangote bayan an masu saukin dakon mai
- Shugaban IPMAN na kasa, Maigandi Garima ya bayyana ranar da za a fara sayar da litar fetur a kan N935
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kungiyar dlillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa za ta rage farashin kowace litar man fetur da 'yan kungiyar ke sayar wa talakawan Najeriya.
IPMAN ta ce farashin man fetur zai koma N935 kowace lita daga Litinin (yau) domin jama'a su samu sauki yayin bukukuwan karshen shekara.
Jaridar The Cable to wallafa cewa za a yi ragin ne bisa sabon tsarin da aka cimma a tsakanin dillalan man fetur da matatar Dangote.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IPMAN ta samu saukin lodin fetur
Jaridar The Nation ta ruwaito shugaban IPMAN na kasa, Maigandi Garima, ya ce sun samu ragin farashin man fetur daga tashar rarraba man fetur ta Dangote.
“Matatar ta fito da sabon tsari na lodawa da farashin da za a rika sayarwa, inda masu sayar da man za su biya farashin N899.50k daga tashar.
“Matatar na gudanar da shirin da nufin tabbatar da cewa an daidaita farashin man fetur a duk fadin ƙasar nan.
Ana gasar rage farashin man fetur
IPMAN ta ce sama da 'ya'yanta 30,000 sun shirya fara loda man fetur daga matatar Dangote da kuma matatar Fatakwal bayan rage farashin lodin mai.
An samu ragin farashin litar fetur a ranar Lahadi zuwa tsakanin N950 da N980 kowace lita a wasu gidajen mai a Lagos, bayan NNPCL da Dangote sun rage farashi.
Matatar Dangote ta fara rage farashin fetur
A wani labarin, kun ji cewa matatar mai ta Dangote ta shiga yarjejeniya da gidan man MRS domin fara sayar wa 'yan Najeriya kowace litar fetur a kan farashin N935.
Matatar ta yi ragin bayan kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya sanar da rage farashin man feturinsa zuwa kimanin N899 albarkacin bukukuwan karshen shekara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng