Matashi Ya Mutu a Hannun Yan Sanda, Basarake a Arewa Ya Bukaci Kaddamar da Bincike

Matashi Ya Mutu a Hannun Yan Sanda, Basarake a Arewa Ya Bukaci Kaddamar da Bincike

  • Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci yan sanda su binciki mutuwar Jimoh AbdulQodir a hannun jami'ansu
  • Iyalan marigayin sun yi zargin cin zarafi da neman boye gaskiya, suna rokon hukumomi su dauki mataki
  • Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara ta tabbatar da mutuwar AbdulQodir, tana mai cewa za a gudanar da cikakken bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Sarkin Ilorin a jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci bincike kan mutuwar matashi a hannun yan sanda.

Basaraken ya bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya kafa kwamitin bincike kan mutuwar Jimoh AbdulQodir.

Basarake ya bukaci yan sanda su kaddamar da bincike bayan mutuwar matashi a hannunsu
Wani matashi ya rasa ransa a hannun yan sanda, sarkin Ilorin ya bukaci kaddamar da bincike. Hoto: Legit.
Asali: Original

AbdulQodir: Basarake ya bukaci kaddamar da bincike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta ce marigayin ya mutu ne a hannun ‘yan sanda a Ilorin a Kwara a ranar Juma’a 20 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Rai ya yi halinsa: Tsohon hadimin Atiku Abubakar ya kwanta dama

A wata sanarwa da kakakinsa, Alhaji Abdulazeez Arowona, ya fitar ranar Lahadi, Sarkin ya nuna alhininsa kan lamarin.

Ya bayyana mutuwar AbdulQodir a matsayin abin bakin ciki da rashin imani, yana mai cewa matashin ya mutu a yanayi mara dadi.

Sarkin ya jajantawa iyalan marigayin tare da abokan arziki, ya kuma bukaci IGP Egbetokun ya binciki yadda aka yi matashin ya rasu.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro su kiyaye ka’idoji da bin dokoki na kasa da kasa yayin mu’amala da jama’a.

Yadda matashin ya mutu a hannun yan sanda

Rahotanni sun ce an kama AbdulQodir, mai shekara 35, a ranar 19 ga Disambar 2024 kan bashin Naira 220,000, Sai dai an ce ya mutu washegari, 20 ga Disambar 2024 a hannun ‘yan sanda.

Iyalan marigayin sun zargi ‘yan sanda da cewa sun azabtar da shi tare da kokarin rufa-rufa kan lamarin.

Rundunar ‘yan sanda a Kwara ta tabbatar da mutuwar AbdulQodir, tana mai alkawarin gudanar da cikakken bincike.

Kara karanta wannan

An kona makarantar Kandahar a Bauchi: Rigima ta kaure tsakanin matasa da ƴan CJTF

Gwamnan Kwara ya ragewa malama matsayi

Kun ji cewa Gwamnatin Kwara ta rage matsayin malama Fatimoh Nike saboda fada a wajen aiki da kuma lakadawa 'yar NYSC dukan tsiya.

Gwamnatin ta ce za ta tura malamar zuwa wata makaranta tare da ba ta horo kan kyawawan dabi’u domin gyara halayenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.