Rai Ya Yi Halinsa: Tsohon Hadimin Atiku Abubakar Ya Kwanta Dama
- Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Hon. Shima Ayati ya rasu a Makurdi bayan gajeriyar rashin lafiya
- Ayati ya yi aiki tare da Atiku Abubakar a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo kuma ya jagoranci kwamitin tallafin Zaki Biam a 2003
- Marigayin dan asalin karamar hukumar Ukum ta jihar Benue, ya bar siyasa domin mayar da hankali kan kasuwancinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin, Hon. Shima Ayati, tsohon mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar ya rasu a Makurdi.
Tsohon hadimin Atiku Abubakar ya koma ga Allah
Dan uwan marigayin, Ahangba Ayati ya tabbatar da rasuwar marigayin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahangba ya ce Ayati ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda yana mai cewa yana zaune cikin kwanciyar hankali kafin mutuwarsa.
Marigayin ya yi aiki tare da Atiku Abubakar a lokacin gwamnatin Obasanjo na tsawon shekara hudu, kuma aka tsawaita wa’adinsa.
Daga bisani, rikici tsakanin Olusegun Obasanjo da mataimakinsa Atiku ya sa aka cire Ayati daga mukaminsa ba tare da cikakken bayani ba.
Gudunmawar da Ayati ya bayar a Benue
Ayati ya kasance dan siyasa mai matukar kishin al’umma, wanda ya rubuta littattafai da dama kuma ya samu girmamawa a jihar Benue.
Bayan ya bar siyasa, ya mayar da hankali kan harkokin kasuwancinsa, inda ya kasance mutum mai saukin kai da son zaman lafiya.
Danginsa sun bayyana cewa za su sanar da shirye-shiryen jana'iza nan ba da jimawa ba, yayin da jama’a ke jimamin rashin marigayin.
Tsohon alkalin Kotun Koli ya kwanta dama
Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar Mai Shari’a Uthman Muhammad Argungu a matsayin babban rashi ga kasa da kansa.
Mai Shari’a Argungu, wanda ya rasu yana da shekaru 90, an binne shi a Argungu, jihar Kebbi, bisa koyarwar Musulunci.
Shugaba Tinubu ya tuna da rayuwar mai Shari'a, Argungu, wanda ya yi wa Najeriya hidima mai cike da gaskiya da jajircewa.
Asali: Legit.ng