Atiku Ya Gano Manyan Matsaloli 5 a Kasafin 2025, Ya ba Tinubu Muhimmiyar Shawara

Atiku Ya Gano Manyan Matsaloli 5 a Kasafin 2025, Ya ba Tinubu Muhimmiyar Shawara

  • Atiku Abubakar ya ce gibin Naira tiriliyan 13 a kasafin kudin 2025 yana nuna rashin tsari mai dorewa da dogaro kan bashi
  • Dan takarar PDP a 2023 ya soki yadda kudin biyan bashi (N15.trn) ya kusa ya yi daidai da kudin gudanar da ayyukan ci gaba (N16trn)
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya lissafa manyan matsaloli biyar da hango a kasafin kudin 2025 da Bola Tinubu ya gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Atiku Abubakar ya ce kasafin kudin 2025 ba zai iya magance matsalolin tsari da tattalin arzikin Najeriya ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce kasafin 2025 na N48trn da ke hasashen samun kudin shiga na N35trn, ya haifar da gibin N13trn na GDP.

Atiku Abubakar ya yi magana kan kasafin kudin 2025 da Tinubu ya gabatar
Atiku ya ce akwai matsaloli biyar da ya gano a kasafin 2025 da Tinubu ya gabatar. Hoto: @atiku, @officialABAT
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafina na X, Atiku ya ce wannan kasafin ya nuna cewa gwamnatin APC ba ta canja salon kasafin ba tun daga shekarar 2016.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Naira tiriliyan N5.84, an fadi ayyukan da aka yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnatin na shirin karbo rancen sama da N13trn a matsayin bashin da zai hada da N9trn na kai tsaye da kuma N4trn na ayyuka na musamman."

- A cewar Atiku.

Atiku ya kara da cewa:

"Wannan tsarin rancen ya yi kama da na gwamnatocin baya, wanda ke kara nauyin bashin kasa da kuma hadarin biyan riba da tasirin kudaden waje."

Dan takarar PDP a zaben 2023 ya ce babu wata alama da ta nuna cewa kasafin kudin 2025 zai kawo ci gaba mai dorewa ko magance matsalolin tattalin arzikin Najeriya.

Atiku Abubakar ya lissafa wasu matsaloli 5 da ya hango a kasafin 2025:

1. Rashin ingantaccen tubali a kasafin kudin:

Atiku Abubakar ya shaida cewa kasafin kudin 2024 ya gaza yin tasirin azo a gani kuma ya nuna rashin kyakkyawar gudanarwa.

"Har zuwa karshen zangon kudi na uku, kasa da kashi 35% na kudaden da aka ware don manyan ayyukan MDAs aka kashe, duk da ikirarin cewa an aiwatar da kashi 85%.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware N27bn domin rabawa Buhari, Jonathan da mataimakansu a 2025

"Wannan gazawar wajen kashe kudaden da aka ware don ayyukan cigaba, wanda ke da matukar muhimmanci wajen inganta tattalin arziki, ya haifar da damuwa kan aiwatar da kasafin kudin 2025."

- A cewar Atiku.

2. Babban nauyin biyan bashin kudi:

Za a biya bashin da ya kai Naira tiriliyan 15.8 (kashi 33% na dukkan kudaden da aka ware), wanda kusan yayi daidai da kudaden da aka ware don manyan ayyuka (Naira tiriliyan 16).

Haka kuma, biyan bashin ya zarce kudaden da aka warewa muhimma bangarori kamar tsaro (N4.91trn), ababen more rayuwa (N4.06trn), ilimi (N3.52trn), da kiwon lafiya (N2.4trn).

Wannan rashin daidaito na iya dakile zuba jari mai mahimmanci tare da janyo dogaro kan ci gaba da karbar bashi, wanda zai lalata daidaituwar tattalin arziki.

3. Kashe kudaden gwamnati marar dorewa:

Kudaden da ake kashewa na yau da kullum sun yi yawa fiye da kima, inda aka ware sama da Naira tiriliyan 14 kan tafiyar da ma’aikatu da tallafa wa hukumomin gwamnati..

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Rashin daukar matakai na musamman don dakile almubazzaranci da kara ingancin kashe kudaden gwamnati yana kara tsananta matsalolin kasafin kudi.

4. Rashin kudaden manyan ayyuka:

Bayan an cire kudaden biyan basussuka da na gudanarwar gwamnati, abin da ya rage don kashewa a ayyukan ci gaba shi ne kashi 25% zuwa 34% na jimlar kasafin kudin.

Wannan na nufin an warewa kowane mutum kusan N80,000 ($45), wanda ba zai wadatar da bukatun 'yan kasar da ke fama da karancin ci gaba da rashin wadatar ababen more rayuwa ba.

Atiku ya ce wannan kudin ba zai isa ba ya magance gibin ababen more rayuwa a Najeriya da haɓaka al'umma ba.

5. Karin hsaraji da matsin tattalin arziki:

Shawarar gwamnati na daga kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10% mataki ne na koma baya da zai kara tsananta tsadar rayuwa kuma ya hana ci gaban tattalin arziki.

Kara nauyin haraji a kan al’umma da ke fama da matsaloli, ba tare da magance matsalolin shugabanci ba, zai iya kara tsananta wahalhalun tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Farashin shinkafa ya karye daga N84000, an fadi kasuwar da ake samunta da sauki

Tinubu ya karbo bashin Naira tiriliyan 5.84

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta karbo rancen Naira tiriliyan 5.84 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2024.

Ofishin da ke kula da basussuka na Najeriya (DMO) ya yi bayanin cewa gwamnatin ta karbo bashi ne daga kasuwar FGN Bond duk da hauhawar farashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.