Rai Baƙon Duniya: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An tafka babban rashi bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Manjo-janar Godwin Osagie Abbe
- Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024 a Abuja bayan fama da doguwar jinya
- Kafin rasuwarsa, matsayin ya mulki jihohin Akwa Ibom da Rivers a matsayin soja kafin rike muƙamin Minista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a mulkin soja, Godwin Osagie Abbe ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rike muƙamin Ministan Tsaro a zamanin marigayi Shugaban Ƙasa, Umaru Musa Yar'Adua.
Yaushe marigayi tsohon gwamnan ya rasu?
Vanguard ta ruwaito cewa Janar Abbe ya mulki jihar Akwa Ibom daga 31 ga Yulin 1988 zuwa 5 ga Satumbar 1990.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan marigayin ya kuma mulki jihar Rivers daga Agustan 1990 zuwa Janairun shekarar 1992.
Marigayin ya rasu ne a Abuja a ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024 bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Tsohon Manjo-janar ɗin, wanda ɗan jam’iyyar PDP ne, ya kuma rike mukamin Ministan Harkokin cikin gida a zamanin marigayi Shugaba Umaru Yar'Adua.
An haife shi a ranar 10 ga Janairum 1949, kuma zai cika shekaru 75 a duniya a ranar 10 ga Janairun 2025, cewar Daily Post.
Karatu da rayuwar marigayin a gidan soja
Marigayin ya kammala karatun digirin shi na biyu a Harkokin Duniya daga Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife.
Ya kuma samu horo daga Makarantar Sojin Amurka ta Infantry, Fort Benning da Georgia da Kwalejin Sojin Ghana; da Cibiyar Kasa ta Tsare-Tsare da Dabarun Siyasa a Kuru.
A lokacin aikinsa, ya rike mukamin Babban Kwamandan Runduna ta 2 ta Sojojin Najeriya (GOC) da Kwamandan Rundunar Horarwa da Tsare-Tsare (TRADOC) da da Kwamandan Kwalejin Yaki ta Kasa.
Marigayi Janar Abbe ya yi ritaya daga aikin soja a shekarar 1999 da mukamin Manjo Janar.
Jarumin masana'antar Kannywood ya rasu
Kun ji cewa Masana'antar Kannywood ta rasa jarumi Baba Ahmadu, wanda aka fi sani da Hedimasta a shirin Dadin Kowa mai dogon zango.
Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha, ya sanar da rasuwar Baba Ahmadu tare da mika sakon ta'aziyyarsa.
Asali: Legit.ng