Adadin Mutanen da Suka Mutu a Turereniyar Karbar Shinkafar Sadaka Ya Karu zuwa 22
- Adadin mutanen da suka mutu a turmutsitsin Anambra ya kai 22 yayin da har yanzu wadanda suka ji rauni ke a asibiti
- Legit Hausa ta rahoto cewa turmutsitsin ya faru ne a wani filin wasa yayin rabon shinkafa da gidauniyar Obijackson ta shirya
- Ba wannan ne turmutsitsin farko ba a cikin watan Disambar nan, an samu irinsa a birnin tarayya Abuja da kuma jihar Oyo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a turmutsitsin da ya faru a jihar Anambra ya kai 22, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.
Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce sun fara gudanar da bincike kan wannan lamari.
Anambra: Wadanda suka mutu sun kai 22
Ikenga, wanda Sufritandan 'yan sanda ne, ya ce mutane 22 sun mutu yayin da wadanda suka samu raunuka suke karbar magani a asibiti a cewar rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kwamishinan 'yan sanda, Nnaghe Obono Itam, ya ziyarci asibitin da aka kwantar da wadanda turmutsitsin ya shafa, wanda ya faru a ranar 21/12/2024 a Okija da ke Ihiala."
"Kwamishinan ya bayyana alhini ga iyalai da abokan wadanda suka rasu tare da yi musu addu’ar samun juriya, sannan ya yi wa masu jinya fatan samun sauki."
- A cewar sanarwar 'yan sandan.
Turmutsitsi ya halaka mutane a garuruwa
Turmutsitsin ya faru ne ranar Asabar yayin rabon shinkafa a filin wasa na Amaranta da ke Okija, karamar hukumar Ihiala. An shirya taron ne karkashin gidauniyar Obijackson.
Wannan turmutsitsi da ya faru a Anambra ba shi ne na farko ba a baya-bayan nan, kamar yadda aka taba samu a Abuja da Oyo a watan Disamba.
Hukumomi sun yi kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa yayin rabon kayan tallafi domin kauce wa sake faruwar irin wannan al’amari mai ban tausayi.
Mutane da dama sun mutu a Abuja
Tun da fari, mun ruwaito cewa mutane da dama sun mutu yayin da wasu suka jikkata a Maitama da ke Abuja wajen karbar tallafin kayan abinci.
Mutane kusan 10 ne suka mutu ne a wani turmutsitsin da ya afku a cocin Holy Trinity Catholic da ke Maitama, Abuja, wanda ya tada hankalin Shugaba Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng