Baki Har Kunne: Gwamna Ya Amince da ba Sarakunan Gargajiya Tallafin N250,000 Duk Wata

Baki Har Kunne: Gwamna Ya Amince da ba Sarakunan Gargajiya Tallafin N250,000 Duk Wata

  • Sarakunan gargajiya a jihar Abia sun nuna godiya ta musamman da Gwamna Alex Otti da ya amince da ba su tallafi duk wata
  • Gwamna Otti ya amince da ba sarakunan gargajiya N250,000 duk wata domin taimaka musu wurin gudanar da ayyukansu
  • Shugaban kwamitin sarakunan gargajiya, Eze Linus Nto Mbah shi ya tabbatar da haka inda ya ce hakan zai taimaka wurin dakile matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti zai yi wa sarakunan gargajiya gata da tallafin kudi kowane wata.

Gwamnan ya amince da bayar da N250,000 a matsayin kudin tallafin wata-wata ga sarakunan gargajiya a jihar.

Gwamna zai rika ba sarakunan gargajiya N250,000 duk wata
Gwamna Alex Otti ya amince da tallafawa sarakunan gargajiya da N250,000 duk wata. Hoto: Alex C. Otti.
Asali: Twitter

Gwamna Otti ya yi wa sarakunan gargajiya gata

Wannan matakin ya fito ne daga bakin Shugaban Kwamitin Sarakunan Gargajiya a jihar, Eze Linus Nto Mbah, The Nation ta tabbatar.

Kara karanta wannan

'Abin da zai jawo tunkuda keyar sarakunan gargajiya gidan kaso nan take'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin ya bayyana hakan tare da gode wa gwamnan bisa wannan kyauta da ya yi musu inda ya ce zai kara inganta harkokinsu.

Eze Linus Nto Mbah ya bayyana alakar gwamnan da sarakunan gargajiya a matsayin abin yabo.

Ya kara da cewa babu tsohon gwamna da ya taba girmama masarautun gargajiya kamar yadda Gwamna Otti ke yi, cewar Daily Post.

Sarakunan gargajiya sun godewa gwamna Alex Otti

Sarakunan gargajiya sun kuma nuna godiya ga gwamna da amincewa da bayar da kyautar musamman ta Kirsimeti na N150,000 ga kowanne sarki.

Eze Mbah ya roki Allah ya ba Gwamna Otti lafiya da hikima da kuma karfin guiwa don cigaba da tafiyar da al’amuran jihar Abia cikin nasara.

Har ila yau, ya tabbatar da cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da goyon bayan gwamnan wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunansu da kuma yaki da miyagun laifuka.

Kara karanta wannan

Kirsimeti: Gwamna a Arewa ya ware tirelolin shinkafa 100 domin rabawa al'umma

Kirsimeti: Gwamna Ododo ya raba tirelolin shinkafa

Kun ji cewa Gwamna Ahmed Usman Ododo ya tausayawa al'umma a Kogi inda ya raba tirelolin shinkafa ga mutane.

Gwamna Ododo ya dauki wannan mataki ne ganin yadda ake cikin halin kunci da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.