Gwamnatin Tinubu Ta Karbo Bashin Naira Tiriliyan N5.84, An Fadi Ayyukan da Aka Ki
- Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta ciyo bashin Naira tiriliyan 5.84 a 2024 domin cike gibin kasafin kudin shekarar
- Rahoto ya nuna cewa sha’awar masu zuba jari a kasuwar FGN Bonds a 2024 ya kai Naira tiriliyan 7.09 duk da hauhawar farashi
- Duk da hakan, sakamakon gwamnjon kayayyaki da aka yi a kasuwar FGN ya nuna cewa gwamnati na bukatar rancen N5.84trn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta karɓo bashin Naira tiriliyan 5.84 daga kasuwar FGN Bond a 2024 don cike gibin kasafin kudin shekarar.
Wannan adadi ya yi kasa da na shekarar 2023 da ta karɓo rancen Naira tiriliyan 5.85 ta hannun ofishin gudanar da bashi na DMO da kashi 0.17 cikin 100.
Gwamnati ta karbo bashin N5.85trn
A 2022, DMO ta tara Naira tiriliyan 3.06 daga kasuwar FGN Bond kamar yadda sakamakon gwanjon da aka gudanar ya nuna, inji rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun kuma nuna cewa, jimillar kudaden da masu zuba jari suka zuba a kan FGN Bonds a 2024 ya kai Naira tiriliyan 7.09.
Wannan adadi ya yi kasa da na 2023 da ya kai Naira tiriliyan 7.43, saboda masu zuba jari sun fi sha'awar kayan saka hannun jari marasa haɗari.
An samu hauhawar farashi a kasuwar FGN
Jaridar ThisDay ta rahoto cewa DMO ta nemi tara Naira tiriliyan 5.72 a cikin watanni 12 na 2024, amma buƙatar kayan saka hannun jarin ta kai Naira tiriliyan 7.09.
Wannan sha'awar ta karu ne saboda hauhawar farashin kaya mai yawa, wanda ya shafi hukuncin masu zuba jari na cikin gida da na kasashen waje.
An samu gibi sosai kasafin kudin 2024, inda aka samu bambancin kudaden shigar gwamnati da kuma kudaden da za a kashe, wanda ya tilasta Tinubu ya karbo bashin.
Tinubu zai karbo rancen Naira tiriliyan 1.7
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya aikawa majalisar tarayya bukatar amincewa da kudurinsa na karbo sabon rancen Naira tiriliyan 1.7.
Shugaba Tinubu ya shaidawa majisar cewa yana son karbo sabon bashin ne domin ba shi damar cike gibin kasafin 2024 da zai gudana har zuwa cikin shekarar 2025.
Asali: Legit.ng