Gwamna Radda Ya Ziyarci Mutanen da Aka Ceto a Hannun 'Yan Bindiga, Ya ba da Tallafi

Gwamna Radda Ya Ziyarci Mutanen da Aka Ceto a Hannun 'Yan Bindiga, Ya ba da Tallafi

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tuna da marasa lafiya da ke kwance a asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina
  • Radda wanda ya ziyarci a asibitin a ranar Asabar, ya duba marasa lafiya ciki har da matan da aka ceto daga hannun ƴan bindiga
  • Gwamnan bayan duba lafiyarsu ya kuma ba su tallafin kuɗi domin su samu su koma gidajensu bayan an kammala duba lafiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ziyarci majinyata da ke samun kulawa a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Katsina.

Gwamna Radda ya kai ziyarar ne a ci gaba da ƙoƙarin da yake yi na tallafawa waɗanda matsalar tsaro da sauran masu fama da rashin lafiya a jihar ta shafa.

Gwamna Radda ya ziyarci marasa lafiya
Gwamna Radda ya kai ziyara a asibiti Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fita daban a Najeriya, ya ba ma'aikatan gwamnati hutun kwanaki 7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya duba marasa lafiya

A yayin ziyarar ta ranar Asabar, gwamnan ya mai da hankali musamman ga mata tara da aka ceto kwanan nan daga hannun ƴan bindiga, waɗanda ake kula da su a asibitin.

Sanarwar ta ce Gwamna Radda ya kuma jajantawa wata mata da ta haihu a lokacin da ake tsare da ita, ya kuma umarci asibitin da su ba da cikakkiyar kulawa ga dukkanin mutanen da aka ceto daga wajen ƴan bindiga.

Ya kuma ba da tallafin kuɗi domin sauƙaƙa musu komawa gidajensu lafiya bayan an sallame su.

"Gwamna Radda ya nuna kulawa a asibitin, tare da tattaunawa kai tsaye da marasa lafiya, neman jin yadda lafiyarsu take, tare da tabbatar da samun kulawa mai inganci."
"Ya kuma bayar da tallafin kudi domin rage musu nauyin kuɗaden da ake kula da su."

- Ibrahim Kaula Mohammed

Gwamna Radda ya naɗa kwamishina

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kashe N59.4b don farfado da aikin shekaru 24 a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya naɗa sabon kwamishina a cikin gwamnatinsa.

Gwamna Radda ya ɗauko mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kuɗi da bankuna, Malik Anas, ya naɗa shi a matsayin sabon kwamishina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng