Kasafin Kudi: Yadda Gyara Gidajen Tinubu, Shettima Za Su Lakume N6.36bn
- Gwamnatin tarayya ta shirya yin gyara a gidajen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima
- An ware N6.36bn a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka gabatarwa majalisar tarayya domin gudanar da ayyukan
- Daga cikin waɗanda za su amfana da gyaran da za a yi har da masu taimakawa shugaban ƙasan da mataimakinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ware maƙudan kuɗaɗe domin gyara gidajen shugaban ƙasa Bola Tinubu, Kashim Shettima, da wasu mataimakansu a cikin ƙudirin kasafin kuɗin 2025.
Gwamnatin tarayyar dai ta ware Naira biliyan 6,364,181,224 domin gudanar da ayyukan.
Binciken da jaridar The Punch ta yi a kan shirin kashe kuɗaɗen da ke ƙunshe a cikin ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2025 da aka gabatarwa majalisar tarayya ya nuna hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gyara gidajen Tinubu, Shettima zai ci N6.36bn
Binciken ya nuna cewa gyaran da ake yi a fadar shugaban ƙasa a duk shekara zai ci N5.49bn.
A cewar kasafin kuɗin, N765m za a yi amfani da ita wajen gyara kwatas na mataimakin shugaban ƙasa da kuma masaukin baƙi.
Gyaran kwatas ɗin shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasa zai ci N6.39m, yayin da gyaran wuraren tsaro, ɗakunan taro, ɗakin motsa jiki da kwatas na hadiman shugaban ƙasa zai ci N49m.
Wani bincike da aka yi a kan kasafin ya nuna cewa ana sa ran Tinubu da mataimakinsa za su samu N87m a matsayin alawus-alawus na zama, yayin da aka ware N127m domin siyan motocin SUV.
Har ila yau, an ware Naira biliyan 3.66 domin siyan motoci a fadar shugaban ƙasa, sannan kuma za a kashe N1,09bn wajen sauya motocin SUV a fadar gwamnati.
Tinubu, Shettima za su ci N9bn a tafiye-tafiye
A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana kuɗaɗen da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima za su ci domin tafiye-tafiye a 2025.
A cikin kasafin kuɗin shekarar 2025, alƙaluma sun bayyana cewa shugaban ƙasan da mataimakinsa za su laƙume N9bn a tafiye-tafiye da cin abinci.
Asali: Legit.ng